Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na ingiza ci gaban tattalin arziki ta hanyar cudanya a kasuwannin cikin gida da na ketare
2020-08-03 19:48:02        cri

A kwanakin baya ne, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar da wani rahoton bincike, dake bayyana cewa, kaso 99.1 cikin 100 na kamfanonin ketare suna son ci gaba da zuba jari da kuma gudanar da harkokinsu a kasar Sin, shugabannin wasu manyan kamfanonin ketare ciki har da Qualcomm da BCG na Amurka su ma sun nuna imani kan makomar tattalin arzikin kasar Sin, to mene ne dalilin da ya sa wadannan kamfanonin ketare suka cimma matsaya guda kan wannan batu, yayin da ake fuskantar barazanar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19? Dalilan suna yanayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki da kokarin da kasar Sin take domin raya tattalin arziki.

Duk da cewa, a farkon watanni shida na bana, alkaluman dake shafar ci gaban tattalin arziki, da masana'antu, da aikin samar da hidima, da sayayya, da zuba jari a kasar Sin sun ragu, amma mahukuntan kasar Sin sun fahimci yanayin da kasar ke ciki sosai.

Yayin taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka kira kwanan baya, an jaddada cewa, matsalolin da kasar Sin take fuskanta za su kasance na matsakaici ne ko dogon lokaci, don haka ya zama wajibi ta yi kokarin ingiza ci gaban tattalin arziki ta hanyar cudanya a kasuwannin cikin gida da na ketare.

Da farko dai, ya dace a kara mai da hankali kan kasuwannin cikin gidan kasar tare kuma da kara habaka bukatun cikin gida na al'ummun kasar, a baya kasuwannin ketare da albarkatun ketare sun taka babbar rawa kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, amma yanzu tattalin arzikin duniya ya gamu da matsala, a don haka kamata ya yi kasar Sin ta dogara kan kasuwanninta domin dakile rikici da kalubale da take fuskanta.

Abu mai muhimmanci shi ne ba zai yiyu ba a rufe kofa yayin da ake raya tattalin arziki, hanya mafi dacewa ita ce a kara cudanya da kasuwannin kasa da kasa, ta yadda za a cimma burin samun ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci ba tare da rufa rufa ba, hakan shi ma zai kyautata tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa, a karshe har ma a ciyar da tattalin arzikin duniya gaba yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China