Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Falasdinu ta bukaci EU ta dauki ingantattun matakan da za su dakatar da Isra'ila daga aiwatar da shirinta na gini a yankin gabashin birnin Kudus
2020-08-03 11:19:09        cri
Falasdinu ta yi maraba da wasikar da jami'an diflomasiyya na Tarayyar Turai suka rattabawa hannu, wadda ke adawa da shirye-shiryen Isra'ila na gini a wani yankin gabashin birnin Kudus, tana mai bukatar EU ta dauki ingantattun matakai.

A ranar 31 ga watan Yuli ne, wakilan EU da jakadun kasashen Turai 15, suka aike da wasika ga ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila, inda suka bayyana adawarsu da matakin gwamnatin Isra'ilar na fara gini a yankin Givat Hamatos.

Hanan Ashrawi, mambar kwamitin zartarwa na kungiyar 'yantar da al'ummar Falasdinu, ta bukaci jami'an na Turai su dauki matakin da zai hana Isra'ila aiwatar da shirin nata.

Cikin wata sanarwa, Hanan Ashrawi ta ce sun yi ammana cewa, ya kamata Tarayyar Turai da gwamnatocin kasashe 15, su dauki matakan da za su hana Isra'ila ci gaba da ayyukan keta doka da cin zarafi da mamaya. (Faiza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China