Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin da ke kiyaye zaman lafiya a fadin duniya
2020-08-01 21:08:42        cri

Yau 1 ga watan Agusta, rana ce ta cika shekaru 93 da kafuwar rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin. Yau shekaru 93 da suka wuce, rundunar ta kafu da yunkurin neman 'yancin kan al'ummar kasar. Bayan bunkasuwarta cikin shekarun sama da 90 da suka wuce, yanzu rundunar ta zamanto rundunar da ke taka muhimmiyar rawa a fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin duniya, baya ga yadda take kokarin tsaron gida da al'ummar kasar.

A cikin shekaru 71 da suka wuce tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, rundunar sojan kasar ba ta taba ta da yaki ko rikici ba, ba ta kuma taba kai wa wata kasa hari ba, haka kuma ba ta taba mallakar filin wata kasa ba, a maimakon hakan dai, kullum tana bin manufar tsaro ta kare kanta. Kasancewarta kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, kudin da ta kasafta a fannin tsaro ya kai kaso 1.3% na alkalumanta na GDP, adadin da ya yi kasa da kaso 2.6% na matsakaicin kudin da kasashen duniya suka ware a wannan fanni.

A hannu daya kuma, sojojin kasar Sin suna kokarin bada gudummawa a kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a duniya. Tun bayan da kasar Sin ta tura jami'an soja masu sa ido ga MDD karo na farko a shekarar 1990, gaba daya sojojin kasar Sin sun shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya sama da 20 da MDD ta gudanar, kuma yawan sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar ta tura ya kai sama da dubu 40, hakan ya sa ta zama kasar da ta fi samar da sojoji da kuma kudade ga MDD domin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya. A yanzu haka kuma, akwai sojojin kasar Sin sama da 2500 da suke ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, a yayin da wasu 8000 suke cikin shirin ko ta kwana.

Daga cikin ayyukan da sojojin suka gudanar na kiyaye zaman lafiya a sassa daban daban na duniya, tsawon hanyoyin da suka gina ko suka gyara ya kai kimanin kilomita dubu 15, a yayin da gadojin da suka gina ko gyara suka kai sama da 300. Sa'an nan, sojojin sun kuma kawar da nakiyoyi sama da dubu 10 da aka binne a karkashin kasa, tare da yin jigilar kayayyakin da nauyinsu ya kai sama da ton miliyan 1.3. Sojojin sun kuma yi jinyar masu fama da rashin lafiya sama da dubu 200, tare da gudanar da ayyukan sintiri da ba da kariya da samame da sauransu.

A shekarar 2014, cutar Ebola mai saurin kisa ta barke a wasu kasashen yammacin Afirka, kuma bi da bi rundunar sojan kasar Sin ta tura wasu ayarin ma'aikatan lafiya guda shida zuwa kasashen Saliyo da Liberia, inda suka samar da gudummawar jinya ga al'ummar da mummunar cutar ke addabarsu, gudummawar da ta kasance mafi girma da rundunar ta samar ta fannin kiwon lafiya tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin.

Baya ga haka, kasar Sin ta kuma tura ayarorin sojojin ruwa zuwa mashigin tekun Aden da tekun Somaliya, don su ba da kariya ga jiragen ruwa da ke zirga-zirga a yankin, ayarorin da kawo yanzu suka kai 35, wadanda suka ba da kariya ga jiragen ruwa sama da 6700, wadanda kuma suka kiyaye tsari da oda a ruwan tekun.

A sabili da haka ne, sojojin suka samu karbuwa daga MDD da kuma gamayyar kasa da kasa bisa yadda suka gudanar da aiki cikin inganci da kuma sauri. Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix ya bayyana cewa, "cikin shekaru 30 da suka wuce, ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na kasar Sin da suka hada da sojoji da 'yan sanda sun taka muhimmiyar rawa a ayyukan kiyaye zaman lafiya da dama da MDD ta gudanar."

A jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar na taya murnar shiga sabuwar shekarar nan ta 2020, ya ce kasarsa za ta ci gaba da bin hanyar bunkasuwa cikin lumana tare da kiyaye tsaro da ci gaba a duniya. Kamar yadda shugaban ya alkawarta, rundunar sojan kasar Sin za ta ci gaba da kokarin kiyaye zaman lafiya a fadin duniya, don tabbatar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin al'ummar duniya.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China