![]() |
|
2020-08-01 20:03:36 cri |
Wani makiyayi mai suna Suni'er ya bayyana cewa, a da, ba'a iya samun siginar TV a gidansa ba, amma yanzu yana iya kallon fina-finai ta kafar sadarwar Intanet.
A yanzu haka, sama da kaso 95 na makiyayan wurin suna iya jin dadin kyawawan hidimomin da ake samar musu. Wani jami'in dake aiki a kamfanin rediyo da talabijin na jihar Mongoliya ta gida mai suna Xu Liang ya bayyana cewa, kawo yanzu an kammala aikin shimfida layukan sadarwar zamani da tsawonsu ya wuce kilomita 660, kuma gidajen makiyaya sama da 6100 suna iya samun siginar TV.
Ita ma siginar Intanet ta fara shiga cikin gidajen makiyaya. Yanzu akwai makiyaya da dama wadanda suka saka kyamara mai inganci a filayen kiwo. Alal misali, bawan Allah Suni'er yana kiwon raguna sama da 200, inda a cewarsa, duk inda ya je, muddin ya bude wata manhajar dake cikin wayar hannunsa, yana iya ganin ko'ina sarai a filinsa na kiwon raguna.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China