Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Pompeo yana matsa lamba ga kamfanonin Sin bisa hujjar "tsaron kasa"
2020-07-31 21:01:06        cri

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya gabatar da jawabi kwanan baya a jihar California, inda ya sake bata sunan kamfanin kasar Sin wato Huawei, yana mai cewa wai, kamfanin na haifar da barazana ga tsaron kasar Amurka, har ma ba tare da gabatar da dalili ba, Pompeo ya ce kamfanonin Sin ba riba suke nema ba. Irin wadannan furuci na Pompeo, na shaida cewa, Amurka kasa ce dake son yin babakare da keta dokokin kasuwa.

Babban dalilin da ya sa 'yan siyasar Amurka suke nuna damuwa kan ci gaban kamfanonin kasar Sin ciki har da Huawei, har ma suke yunkurin matsa musu lamba shi ne, ba sa son ganin kamfanonin Sin sun shiga sahun gaba a fannin fasahar sadarwar 5G.

A yayin wani taro da aka yi kwanan baya a zauren majalisar dokokin Amurka, an tambayi manyan jami'an gudanarwa daga wasu kamfanonin kimiyya da fasahar kasar uku, wato Apple, da Google da kuma Amazon, cewa ko suna ganin kasar Sin na satar fasahohion kamfanonin Amurka? Wadannan kamfanoni sun amsa da cewa babu shaidu kan hakan, amsar da kuma ta kunyata Pompeo, da ma sauran wasu 'yan siyasar Amurka wadanda ke yunkurin matsawa kamfanoin Sin lamba. Kaza lika hakan ya shaida cewa, su makaryata ne kawai.

A wadannan shekaru, kamfanonin kasar Sin suna ta yin hadin gwiwa da takwarorinsu na Amurka, wadanda suka taimaka sosai ga habakar tattalin arzikin kasar, da samar da karin guraban ayyukan yi. To sai dai kuma sakamakon yadda 'yan siyasar Amurka ke kafa shingaye ga kamfanonin Sin, yawan jarin da Sin ta zubawa Amurka ya ragu ainun.

Scott Kennedy, wani kwararre ne game da hada hadar kasuwancin da Amurka ke yi da kasar Sin. Ya kuma nuna cewa, katse hulda, da mu'amala da kasar Sin, wani babban kuskure ne ga tattalin arzikin Amurka, wanda kuma zai illata tsaron kasar. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China