Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasa da kasa na fatan amfana daga tsarin shawagin taurarin dan Adam na Beidou-3
2020-07-31 21:01:06        cri





Tsarin shawagin taurarin dan Adam na Beidou, ya kasance tsari mafi girma, kuma mafi ingancin hidima da kuma shafar rayuwar al'ummar da kawo yanzu kasar Sin ta kafa a sararin samaniya. Haka kuma, abun more rayuwa na farko ne da kasar Sin ta kafa a sararin samaniya da nufin samar da hidimomi ga al'ummar duk duniya. Tuni aka yi amfani da tsarin a kasashe da dama da suka amsa shawarar ziri daya da hanya daya, kuma bayan da aka kaddamar da tsarin Beidou-3, karin al'ummar duniya na fatan amfanawa da shi.

Tun a shekarar 2014, tsarin shawagin taurarin dan Adam na Beidou ya gama birnin Karachi na kasar Pakistan, da kuma sassan da ke kewayensa, tsarin da ke taimakawa kasar wajen gudanar da aikin safiyo da kulawa da filayen kasar, da tashoshin jiragen ruwa. Babban editan Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Pakistan Syed Paras Ali ya bayyana cewa,"Tsarin Beidou ya fi inganci a fannin taswira idan an kwatanta da sauran tsaruka irinsa. An fara yin amfani da tsarin ne wajen yin safiyo a birnin Karachi. Daga baya mun yi amfani da shi a fannin aikin noma na zamani. Tsarin na iya samar da bayanai masu inganci, wanda ya fi yadda mutane ke safiyo kwarai."

A kasar Myanmar, safiyon aikin ban ruwa na gonakai na da muhimmanci kwarai da gaske. Shugaban sashen kula da aikin gona da kididdigar hukumar aikin noma a bangaren kudancin Yangon, Nyi Nyi Latt ya bayyana cewa, tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 yana da amfani sosai ga kasar Myanmar, wata babbar kasa a fannin aikin noma. Ya ce, "Mun soma amfani da na'urori bisa tsarin shawagin tauraron dan-Adam kirar kamfanin CHCNAV na birnin Shanghai na kasar Sin ne, tun daga shekarar kimanin 2013 ko 2014, ciki har da na'urar karbar bayyanai da wadanda ake iya rike da hannu, muna amfani da su kan aikin yin safiyo, musamman ma a fannonin auna fadin kasa, da tsara taswira, da tattara bayanai da kididdiga game da gonakai da dai sauransu. Wadannan na'urorin sun ba da taimako sosai ga hukumarmu da ma daukacin tsarin safiyo."

Tsarin shawagin tauraron dan Adam na BeiDou-3 yana gudanar da hadin-gwiwa da sauran wasu tsare-tsaren shawagin tauraron dan Adam na duniya, domin su yi aiki tare na kara samar da ingantacciyar hidima ga al'ummar duk duniya. Wani malami daga kwalejin koyon ilimin zirga-zirgar jiragen sama ta Moscow dake kasar Rasha, Sergey Akhramovich yana ganin cewa, tsarin BeiDou zai kara kawo alfanu ga masu amfani da shi a duniya, inda ya ce,"Wannan shi ne babban ci gaba ga kasuwar na'urorin jagorancin zirga-zirga ta hanyar tauraron dan Adam, saboda a halin yanzu, kusan dukkan na'urori, kamar wayar salula, da na'urorin jagorancin zirga-zirga bisa taimakon tauraron dan Adam, suna karbar sakwanni daga tsare-tsaren shawagin tauraron dan Adam daban-daban a lokaci guda. Wato, tsare-tsare biyu sun fi tsari daya kacal amfani wajen bada jagoranci ga zirga-zirga. Ke nan idan kasar Sin ta iya shigar da tsarinta na BeiDou cikin tsare-tsaren duk duniya, za ta bayar da babbar gudummawa ga duniya."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China