Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsarin aikin tauraron dan Adam na beidou-3 ya bude sabon babi a fannin ba da hidima ga daukacin al'ummar duniya
2020-07-31 20:51:25        cri
Da safiyar yau Jumma'a ne aka gudanar da bikin kaddamar da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 a hukumance.

Da yake amsa tambaya game da hakan, yayin taron manema labarai da aka gudanar a yau Juma'a, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce al'ummar Sinawa na matukar alfahari da jin dadi game da wannan nasara, duba da cewa tabbas, tsarin aikin tauraron na Beidou zai amfani daukacin bil Adama.

Wang Wenbin ya kara da cewa, "Mu kan ce Beidou ba na kasar Sin ne kadai ba, tsarin aikin tauraron dan Adam ne na duniya baki daya. Kuma ba kasar Sin kadai zai yi wa aiki ba, zai ba da hidima ne ga duniya baki daya. Bayan kaddamar da tsarin Beidou, zai baiwa masu amfani da shi a dukkanin sassan duniya hidimar taswira, da hidimar sadarwa ta kananan sakwanni, da hidimar ba da agaji a matakin kasa da kasa.

A yanzu haka, hidimar tsarin aikin Beidou ta karade sama da kasashe da yankunan duniya 200, inda mutane sama da miliyan 100 ke cin gajiyar hidimominsa a kullum. Kusan sama da rabin kasashen duniya na amfana daga hidimomin da tsarin na Beidou ke samarwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China