Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
"Kar ki yi kuka, diyyata. Zan je in taimakawa mutane"
2020-08-01 16:32:18        cri

A cikin wannan hoto, wata mace ta rungumi wata yarinya wadda ke kuka. Me ya same su? Ashe, a jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, inda iyalai kan taru, hafsa Wu Yali, wadda ke aiki a jami'ar koyon ilmin likitanci ta sojan kasa ta kasar Sin, ta samu wani umurnin shiga kungiyar ma'aikatan jinya da aka tura birnin Wuhan, inda annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta fi kamari a can baya. Amma diyyarta ba ta so ta tafi, shi ya sa take kuka. Wu Yali ta gaya mata cewa, kar ki yi kuka, diyyata. Zan je in taimakawa mutane. Ta daga fuskar diyyarta, ta goge mata hawayen. Hoton ya burge mutane da yawa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China