Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin kiyayen zaman lafiya da Sin sun ba da babbar gudunmowa ga aikin kiyayen zaman lafiya a duniya
2020-08-01 16:32:09        cri

Yawan sojojin kiyayen zaman lafiya da Sin ta tura kasashe daban daban ya kai fiye da dubu 40. Tun daga shekarar 1990,Sin ta fara tura masu sa idon kan aikin soja zuwa MDD. Ya zuwa yanzu, sojojin jama'ar kasar Sin fiye da 2500 suna aikin wanzar da zaman lafiya a duniya, yayin da wasu 8000 kuwa suna jiran umurni. A cikin wadannan shekaru 30, sojojin kiyayen zaman lafiya a matakai daban-daban sun samarwa jama'ar wuraren dake fama da rikice-rikice zaman lafiya da makoma mai haske,tare da samar da babbar gudunmowa ga aikin kiyayen zaman lafiya a duniya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China