Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
KOMAWA GASAR ZAKARUN SIN ALAMA CE MAI KYAU GA FANNIN WASANNIN KASAR
2020-07-31 09:06:14        cri

Masu sharhi a fannin wasanni, na bayyana muhimmancin komawa buga gasar zakarun kwallon kafar kasar Sin ko CSL na shekarar nan ta 2020. Bayan daukar mataki cikin matsi daga hukumar shirya gasar, an amince a koma buga wasannin gasar tun daga ranar 22 ga watan Yuli, bayan kalubalen cutar numfashi ta COVID-19 da aka fuskanta a birnin Dalian na lardin Liaoning, daya daga wuraren da ake buga wasannin. Daga karshe dai an buga wasan farko na kakar wasannin a wannan birni a ranar 25 ga watan na Yuli.

Kafin hakan, hukumar kwallon kafa ta kasar Sin CFA, ta alkawarta cewa, za a koma buga wasannin ne kadai, idan an tabbatar da samuwar muhallin tsaron lafiya mai inganci. An amince komawa buga wasannin ne, bayan da a baya ake ganin hakan na tattare da kalubale, amma daga baya aka tabbatar da matakin, kasancewar an tanadi matakai da dama, ciki hadda na kebe wadanda ke cikin barazanar harbuwa da cutar, da lura da hanyoyin samar da abinci, tare da maimaita gwajin cutar yadda ya kamata.

Da yake tsokaci kan irin matakan da aka tanada, jami'i mai lura da shawo kan cutar ta COVID-19 a hukumar CSL Qi Jun ya ce "mun lura da yanayin da ake ciki yayin da muke shirya komawa gasar, abun da muke bukata kawai shi ne ci gaba da gudanar da aiki, da gwaje gwaje sannu a hankali".

Sh kuwa sakataren hukumar ta CFA Liu Yi cewa ya yi, kafin CSL ta ayyana fara buga wasannin, hukumar kula da kwallon kafar kasar Sin ta gayyaci manyan masana a fannin yaki da cututtuka, ta kuma gama yin bincike a birane 9 da ake buga gasar cikin su, kafin zabar birnin Dalian da Suzhou na lardin Jiangsu, kana an fitar da kundi mai shafuka 132, dake kunshe da ka'idojin komawa gasar.

Liu Yi ya ce matakin komawa gasar da CSL ta amincewa, yana da matukar daraja. Yayin da fannin wasanni na kasar Sin ke kara farfadowa daga komadar da ya fuskanta, sakamakon barkewar wannan annoba.

Yanzu haka wata daya ke nan, tun bayan da hukumar kwallon kwando ta kasar Sin CBA, ta koma buga wasannin da take jagoranta, tun bayan bullar cutar ta COVID-19 da ta tilasa tsayar da dukkanin al'amura.

CSL dai na fatan nuna kyakkyawan misali ga dukkanin masu kallon gasar kwallon kafar kasar Sin, na yadda biranen kasar ke samar da daidaito tsakanin wasanni, da kuma kalubalen farfadowa daga wannan annoba.

Idan dai har tsarin da aka tanada ya yi nasara, ana iya amfani da dabarun na kasar Sin, wajen ci gaba da buga gasanni a sauran sassan duniya. Hakan zai kuma karfafa gwiwar gwamnati, wajen kara fadada hanyoyin ci gaba da gudanar da sauran fannonin wasanni.

A daya bangaren kuma, cikakkun dabarun da ake bi wajen dawo da harkokin kwallon kafa ajin kwararru ta Sin, tare da nau'oin matakan kariya da ake dauka, da tarnaki da hakan ke haifarwa ga fannin, zai baiwa CSL da sauran masu ruwa da tsaki damar sake duba game da ka'idojin gudanar da wasan na kwallo.

A cewar shugaban hukumar CFA Chen Xuyuan,"duk da irin wadannan wahalhalu, dole mu martaba, tare da kiyaye yanayin tsarin gudanar da kwallon kafa na ainihi.

Baya ga batun tsauraran matakan dakile bazuwar cutar COVID-19 da ake aiwatarwa a wannan gasa karkashin CSL, wadanda suka shafi sauran rukunonin gasanni da ake gudanarwa a kasar, tsarin tafiyar da gasannin ma ya banbanta.

Kamar dai a salon CBA, sauran gasannin ma sun samu dama ta tsara yanayi mafi dacewa, na komawa buga wasanni, karkashin dabarun kaucewa hadurra da ka iya biyo bayan tafiye tafiye tsakanin birane a wannan babbar kasa.

Kaza lika irin wannan salo zai baiwa 'yan wasa da ma'aikata a fannin kwallon kafar, damar samun saukin gudanar da wasa tsakanin kungiyoyi daban daban.

Yayin wata ganawa da Mr. Chen Xuyuan, jami'in ya ce an dauki wannan mataki ne, saboda CFA ta lura da rashin yiwuwar kammala dukkanin wasanni zagaye 30 na kakar cikin watanni 4.

Baya ga sauya tsarin wasanni, tsara gudanar da zagayen wasanni 2, da fara gudanar da zagaye na 2 cikin yanayi mai sauki, ya samar da 'yar dama ta aikin zabo 'yan wasa da za su bugawa tawagar kasar.

A bayyana ne take cewa, wannan salo ya yi daidai da darasin da aka koya, daga salon gasar kwallon kafar kasar Japan rukunin J-League, wadda aka zarga da rashin ba da dama ga gasannin da suka shafi tawagar kasa.

Chen ya ce "Sake komawa buga wasannin kwallon kafa ajin zakarun kasar Sin, zai nunawa duniya sabon yanayin da harkar kwallo ta kasar Sin ke ciki". Ya ce ga alama tsarin gasar CSL zai kasance mafi cikakken tsarin da'a, idan an kwatanta da takwarorin sa na sauran sassan duniya.

Domin tabbatar da daukacin kungiyoyi da 'yan wasan dake buga gasar na cikin kyakkyawan yanayi cikin watanni 2 da za a shafe ana taka leda, kulaflika da yawa sun tsara matakan tabbatar da dakile tsoma hannun wasu sassa na wajen kungiyoyin. Ta yadda 'yan wasa za su kasance cikin nutsuwa, da maida hankali ga samun horo. Duk da cewa 'yan kallo ma kan samar musu da wani nau'in kuzari a lokacin buga wasa.

A daya bangaren kuma, mashirya gasar sun yi kyakkyawan shiri na baiwa 'yan wasan tallafin karfafa tunani, da nishadantar da su, da sauran abubuwa da za su karfafa musu gwiwar kammala wasannin su cikin managarcin yanayi.

Wani bangaren mai armashi ma shi ne, yadda a yanzu kungiyoyin kwallon kafar suka samu karin dama ta kashe kudaden su yadda ya kamata. Hakan ko shakka ba bu, zai yi kyakkyawan tasiri ga kungiyoyin, a gabar da ake ci gaba da yaki da wannan annoba.

Kamar dai yadda CSL ta yiwa komawar ta wasanni lakabin – Kunna zukata biliyan – mafi muhimmanci ga burin CSL shi ne, hukumar ta iya taka muhimmiyar rawa wajen nishadantar da al'umma, duba da cewa, an shafe kusan rabin shekara ana kamfar harkokin wasanni, da sauran hanyoyin nashadantar da al'umma.

A rana ta farko ta taka leda, yawan masu kallo kai tsaye ya shaida cewa, CSL ta cimma burin karkato tunanin masu sha'awar wasanni na kasar Sin da gagarumin rinjaye. A wannan lokaci kuma da fasahar watsa shirye shirye ta 5G, da hanyoyin sadarwa na yanar gizo, da nuna wasanni ta dabaru TIFO, 'yan kallo na kara taruwa cikin nishadi, da karsashin kallon wasanni, tamkar suna cikin filayen da ake gudanar da wasannin a zahiri.

Jin dadin wasanni da CSL ke shiryawa, wata hanya ce ta kawar da kewa da ake fama da ita cikin tsawon lokaci. Kuma wata kila, hakan zai zamo wata dama ta sake dinkewa, tsakanin masu sha' awar kwallon kafa da kulaflikan da suke goyawa baya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China