Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Pompeo na tilastawa kamfanonin Amurka katse hulda da kasar Sin
2020-07-30 21:39:34        cri

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya gabatar da jawabi a kwanan baya a jihar California, inda ya bata sunan kasar Sin, yana mai cewa, wai Sin tana yiwa kamfanonin Amurka matsin lamba, har ma a cewarsa, kamfanonin Amurka wadanda ke kasuwanci da kasar Sin, suna kokarin "farantawa jam'iyya mai mulkin kasar Sin rai", abun da ya sa Sin ke cin zarafin Amurka.

Idan mun dubi misalin da Mike Pompeo ya yi amfani da shi wajen bata sunan kasar Sin, za mu iya gano cewa, maganarsa abun dariya ne kawai. Pompeo ya tsamo maganar mashawarcin Donald Trump kan harkokin tsaron Amurka wato Robert C. O'Brien ne, wanda ya ce, kamfanonin Amurka da dama, ciki har da babban kamfanin kula da harkokin otel-otel na Marriott, da kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na American Airlines, da Delta Airlines, da kuma United Airlines, sun cire kalmomin da suka shafi Taiwan a shafinsu na Intanet, domin kar su hadu da fushin kasar Sin.

Sanin kowa ne cewa, Taiwan, wani yanki ne da ba za'a iya balle shi daga cikin kasar Sin ba, kuma kamfanonin Amurka kamar American Airlines da sauransu, sun ayyana yankin Taiwan a matsayi daya da kasar Sin, al'amarin da ya saba manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Kamar abun da kakakin kamfanin American Airlines ya fada ne, surufin jiragen sama sana'a ce da ta shafi duk duniya, don haka ya zama dole a mutunta ka'idojin kasashen da jiragan saman suke ratsawa.

Ke nan, ina dalilin da ya sa kamfanonin Amurka suke son gudanar da ciniki tare da kasar Sin? Dalilin dai shi ne, tun bayan da aka kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen Sin da Amurka, cimma moriyar juna yana gaban komai a fannin harkokin tattalin arziki da kasuwancinsu.

A 'yan shekarun nan, yawan kudin shigar da kamfanonin Amurka suka samu ta hanyar yin ciniki da Sin ya kai dala biliyan 700 a kowace shekara. Kana kuma, akwai karin kayayyaki kirar kasar Sin masu inganci da rahusa, wadanda suka shiga cikin Amurka, domin kyautata zaman rayuwar al'ummar kasar.

Manazarta na ganin cewa, duk da cewa, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, 'yan siyasar Amurka na cewa ya kamata a katse mu'amala da kasar Sin, amma akasin hakan, Amurka na kara dogaro kan kasuwa gami da kaya kirar kasar Sin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China