Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bayanai game da yadda Sinawa ke kokarin raya aikin gona da kawar da talauci
2020-07-31 10:19:37        cri

 

A kwanakin baya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya kai rangadi a gundumar Li Shu dake birnin Si Ping na lardin Jinlin, wadda ta kasance a arewa maso gabashin kasar. A wannan gunduma, ana samun cibiyar noman masara mafi girma a kasar ta Sin. Dalilin da ya sa shugaban ya yi ziyara a wurin, shi ne domin neman sanin yanayin da ake ciki a fannonin samar da hatsi, gami da amfani da albarkatu masu alaka da aikin gona.

Sinawa su kan ce, "Idan jama'a suna samun isashen abinci, to, ba za su damu ba". Bayan fara samun cutar COVID-19 a kasar Sin, shugaba Xi na kasar ya jaddada a wurare daban daban cewa, yayin da ake fuskantar kalubale, kamata ya yi a kara kokarin raya aikin gona, don tabbatar da tsaro a fannin samar da abinci.

Wannan rangadin da shugaba Xi Jinping ya yi a gundumar Li Shu ya ba shi damar fahimtar ci gaban da aka samu a wannan wuri, musamman ma a fannin raya aikin gona. Cikin shekaru 30 da suka wuce, sakamakon yadda mutanen gundumar Li Shu ba su san wata fasahar mai kyau ta kula da gonakinsu ba, wani irin laka dake cikin gonakin ta ragu sosai, har ma kaurinta ya ragu da kimanin centimita 40. Daga bisani, wani shehun malami na jami'ar aikin gona ta kasar Sin, mai suna Li Baoguo, da sauran wasu kwararrun masanan ilimin aikin gona, suka je gundumar Li Shu, inda suka koyar wa manoman wurin fasahar noma ta zamani. Fasahar da ake amfani da ita a gundumar ta shafi shimfida karan masara a cikin gonaki, har sai sun lalace, sun zama taki, wadanda za su taimakawa aikin gona sosai.

Da ma a gundumar Li Shu ana samun isashen hasken rana, da wani yanayi mai damshi, da gonaki masu kyau, wadanda suka zama sharuda masu kyau domin a gudanar da aikin shuka masara a can. Sa'an nan bayan da aka fara daukar wasu fasahohin zamani a fannin aikin gona, harkar samar da amfanin gona ta kara samun ci gaba a gundumar. A shekarar 2017, an kafa wata babbar cibiyar samar da masara a Li Shu, wadda fadinta ya kai fiye da eka dubu 60. Wannan cibiyar aikin gona ta shafi kauyuka 219, wadda ta samar da guraben aikin yi ga manoma na magidanta 83,981. Ta hanyar hada kan kungiyoyin manoma da kamfanoni, ana sa ran baiwa manoman wurin karin kudin shiga da ya kai fiye da kudin Sin RMB Yuan miliyan 25.

Lu Wei, manomi ne, mai shekaru 52 dake zaune a gudumar Li Shu. Wannan dattijo shugaba ne na wata kungiyar hadin gwiwar manoma. Tun tuni ya fara rungumar ra'ayin kafa babbar cibiyar aikin gona, domin a ganinsa, ta wannan hanya, za a iya hada gonaki a waje guda, sa'an nan a yi amfani da wasu manyan na'urori na zamani don taimakawa aikin gona. Ya kafa kungiyarsa ta hadin kan manoma a shekarar 2011, bisa manoma na magidanta 6. Zuwa yanzu kungiyarsa ta kunshi magidanta 176, wadanda suka mallaki manyan na'urorin aikin gona 54, gami da gonaki da fadinsu ya kai eka 690.

A wannan rangadin da shugaba Xi Jinping ya yi a gudamar Li Shu, shugaban ya ziyarci kungiyar hadin kan manoma ta malam Lu Wei, don gane ma idanunsa yadda ake amfani da na'urorin zamani wajen gudanar da aikin gona. Shugaban ya ce, ya kamata a kara kafa manyan cibiyoyin aikin gona don samar da hatsi masu inganci, kan farashi mai rahusa. Sa'an nan ya kamata a yi amfani da karin manyan na'urorin zamani, da fasahohin noma masu inganci, don kara zamanintar da fasahar aikin nona a kasar Sin, tare da samar da karin kudin shiga ga manoman kasar.

Jama'a, mun san cewa, kasar Sin wata babbar kasa ce da yawan al'ummarta ya kai fiye da biliyan 1.4. Saboda haka, aikin samar da hatsi ya shafi tsaron abinci na kasar, gami da tsaronta a fannoni daban daban. Wannan dalili ya sa kasar ba ta taba yin sakaci ba a kokarinta na raya aikin gona. Wannan rangadin da shugaba Xi Jinping ya yi a wata babbar cibiyar samar da masara shi ma ya shaida yadda shugaban yake mayar da cikakken hankali kan aikin gona na kasar.

Aikin kau da talauci wani babban aiki ne da kasar Sin take kokarin aiwatar da shi, ganin yadda gwamnatin kasar ta yi alkawarin fid da dukkan matalautan kasar daga kangin talauci a wannan shekarar da muke ciki. Sai dai don cimma wannan buri, dole ne a kula da aikin likitanci da kyau, domin akwai mutane da yawa da suke cikin mawuyacin hali sakamakon rashin lafiya. Da ma rashin lafiya ya kan hana mutum aiki, da rage masa damar samun kudin shiga. Sa'an nan ganin likita ya kan bukaci kashe kudi masu dimbin yawa, wanda shi ma ya kan tsananta yanayin talauci da ake fama da shi. Wata kungiyar likitoci dake ba da taimako ga matalauta a kudancin jihar Xinjiang ta kasar Sin ta zama wata shaida kan yadda kasar Sin take kokarin kyautata hidimomin aikin likitanci don taimakawa matalauta.

Kauyen Hong Xing na gundumar Shu Le, dake karkashin garin Kashgar na jihar Xinjiang, ya kasance a bakin babbar hamadar Taklamagan. A bara, an cire kauyen Hong Xing daga jerin sunayen kauyukan kasar Sin masu fama da talauci. Sai dai har yanzu akwai wasu magidantan kauyen da suke fuskantar yiwuwar komawa cikin yanayin talauci, sakamakon yadda wasu daga cikin iyalansu ke fama da rashin lafiya. Saboda haka wannan kauyen ya zama wani wurin da wata tawagar likitoci ta kan ziyarta.

Wannan tawagar ta kunshi likitoci 9, wadanda dukkansu ke aiki a wani babban asibitin dake birnin Urumuqi, wato hedkwatar jihar Xin Jiang. Sun kware a fannonin kula da masu fama da cututtuka masu alaka da hanta, da kashi, da aikin tiyata, da dai sauransu. Kimanin shekaru 2 da suka wuce, wadannan likitoci suka fara kulla hulda da mutane 1067 na magidanta 266 na kauyen Hong Xing, inda suke ba da kulawa ta musamman ga mutane masu fama da talauci.

Zhuang Shihua, daya ne daga cikin likitocin, kuma kwararren likita a bangaren cututtuka masu alaka da hanta. Ya ce, a cikin kauyen Hong Xing, idan sun ga wani mutum maras lafiya, wanda za a iya masa tiyata don warkar da shi, to, za su kai shi asibitinsu, don a yi masa tiyata ba tare da karbar kudi ba. Sa'an nan za su gayawa mutumin sunayen magungunan da ya kamata ya dinga sha a nan gaba.

Maryam Nisa Yassin, wata tsohuwa ce dake zama a cikin kauyen Hong Xing. Ta gaya ma wakilinmu cewa, "Ba mu da isashen kudi domin zuwa ganin likita a birnin Urumqi. Amma wannan tawagar likitoci ta taimaka mana sosai, inda suka ba mu kulawa, da samar mana da magunguna. Hakan ya sa lafiyarmu ta farfado sosai."

A nasa bangare, Roza Apizi yana da matsala a kashin kwankwasonsa, lamarin da ya sa ya kasa ayyukan gona. Ganin yadda matarsa ke shan wahala matuka wajen kula da aikin gona, da yara, da kuma tsoffi, ya sa shi bakin ciki sosai, har ma ya kusan daina neman samun jinya. Sai dai zuwan tawagar likitoci cikin kauyensa ya ba shi sabbin damammaki. Inda likitocin suka taimaka masa neman samun tallafi, daga bisani aka kai shi birnin Urumqi don a yi masa tiyata da jinya a kyauta. A cewarsa, likitoci sun karbe shi a filin jirgin sama, sa'an nan an yi masa tiyata cikin kwanaki 15. Dukkan sassan daban daban sun ba shi kulawa yadda yake bukata. Zuwa yanzu, Roza Apizi ya riga ya warke daga cutar da ya yi fama da ita, sa'an nan ya samu damar gudanar da sauran ayyuka don neman samun karin kudin shiga, lamarin da ya ba shi damar fid da kansa daga kangin talauci.

Ban da kula da majiyyata, wannan tawagar likitoci na kula da wani aiki na daban, wato horar da likitocin da suke aiki a cikin kauyuka. A cewar likita Zhuang, duk lokacin da suka shiga cikin kauyukan, su kan yi kokarin koyar da sabbin fasahohin aikin likitanci ga wasu likitoci na kauyukan, ta yadda za su samu kwarewar aiki, da kula da jama'ar wurin yadda suke bukata.

An ce, a wadannan shekarun da suka wuce, wannan tawagar likitoci ta ziyarci kauyuka daban daban dake jihar Xin Jiang, da kula da jama'a da yawansu ya kai dubu 68, gami da taimakawa horar da likitoci kimanin 100.

Ban da kula da lafiyar jama'a, wata hanya ta daban da Sinawa suke bi wajen taimakawa matalauta, ita ce aikin ilimi. Idan matasa sun samu ilimi, to, za su samu karin damammaki na aiki. Sa'an nan idan suna da aikin yi, to, da wuya su fada cikin wani yanayi na fama da talauci.

Yankin Liangshan dake kudu maso yammacin lardin Si'chuan na kasar Sin, wani yanki ne da aka fi samun 'yan kabilar Yi. Da ma a shekarar 2018, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya taba rangadi a wannan yanki, inda ya ziyarci gidajen wasu mutanen da suke fama da talauci. Zuwa yanzu, lokacin da wakilinmu ya ziyarci kauyen San He na yankin Liangshan, ya ga wasu sabbin gidaje masu kyan gani da aka gina cikin yankin mai tsaunuka. A gidan dan kauyen mai suna Jihoyequ, diyarsa ta biyu ta nuna ma wakilinmu wani sabon dakinta da yayarta.

A lokacin da shugaba Xi Jinping ya ziyarci mutane masu fama da talauci dake cikin yankin Liangshan, a wasu shekaru 2 da suka wuce, Jihoyequ da iyalinsa suna zama a cikin wani tsohon gidan da aka gina shi da laka. A lokacin, shugaban na kasar Sin ya jaddada bukatar kaurar da masu fama da talauci zuwa wani wurin da za su iya samun mahalli mai kyau, don neman fid da su daga kangin talauci. Sa'an nan don aiwatar da manufar da shugaban ya gabatar, an kafa wasu sabbin ungwanni guda 9 a kauyen San He, musamman ma domin karbar mutanen da aka kaurar da su. Ya zuwa watan Mayun bana, an kaurar da dukkan mutane 801 na magidanta 147 masu fama da talauci na kauyen cikin sabbin gidaje. Daga bisani, Jihoyequ da ya kan yi ayyuka daban daban cikin himma da kwazo, ya kafa wani kanti mai sayar da abinci a gaban gidansa, gami da kokarin halartar wasu ayyukan da hukumar kauyen ta tsara, wadanda suka hada da kiwon shanu, da kaza, da zuma, da dasa itatuwa masu samar da 'ya'ya, lamarin da ya sa ya samu karin kudin shiga, har ma kudin ya ninka na baya har sau 5. A cewar Jihoyequ, mutanen kauyen sun samu sabbin gidaje, da kudin shiga, don haka sun samu damar kyautata zaman rayuwarsu sosai. Suna godiya ga gwamnati, kan yadda take ba su kulawa, sa'an nan sun dau niyyar kara kokarin aiki, don neman samun zaman rayuwa mai walwala.

A shekarar 2019, kudin da kowane mutum dake cikin magidanta masu fama da talauci na kauyen San He ya samu ya kai Yuan dubu 10, don haka ana kyautata zaton ganin fid da dukkan mutane masu fama da talauci na kauyen daga kangin talauci a wannan shekarar da muke ciki.

Bayan mutanen kauyen sun samu karin kudin shiga, zaman rayuwarsu na yau da kullum shi ma ya canza. Matar Jihoyequ ta koyi fasahar karbar kudi ta wata manhajar salula da ake kira Wuchat, a cikin kantinta. Sa'an nan abinci da su kan ci shi ma ya canza, domin uwargidan Jihoyequ ta koyi sabbin fasahohin girki, a lokacin da ta halarci wani kwas na koyar da fasahohin dafa abinci.

Sa'an nan wani abun da ya fi faranta ran Jihoyequ da matarsa, shi ne ganin yaransu 5 sun shiga makaranta a matakai daban daban, inda ake koyar musu ilimi a kyauta, wato ba tare da karbar kudi ba.

Lokacin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ziyarci yankin Liangshan, wasu shekaru 2 da suka wuce, ya ce dole ne a kula da aikin bada ilimi yadda ake bukata, don kar a bar yaran dake cikin kauyukan yankin a baya, yayin da ake koyar da ilimi masu amfani ga yaran wurare daban daban.

Madam Abiniuniu wata malama ce dake aiki a wata makarantar kananan yara, wadda har yanzu ba ta manta da maganar da shugaba Xi ya fada mata ba. Inda shugaban ya ce aikin kula da kananan yara na wurin ya dogaro a kan ta. Wannan magana ta sa Madam Abiniuniu kara nuna himma da kwazo matuka, yayin da take kula da kananan yara, da koya musu ilimi a fannoni daban daban. A cewarta, gwamnati na ta kokarin zuba kudi ga bangaren aikin koyarwa, don neman raya aikin ilimi, da taimakawa kokarin rage talauci. Ganin haka ya sa malamai samun kwarin gwiwa wajen kula da kananan yara, da koyar da su.

Yanzu ana gudanar da wani shiri na kafa wata makarantar kananan yara a duk wani kauyen dake yankin Liangshan, inda ake koyar da ilimi ga yaran ba tare da karbar ko kwabo ba. Madam Abiniuniu ta gaya ma wakilimmu cewa, ganin yadda yaran ke samun ci gaba sannu a hankali ya kan sa ta alfahiri sosai. Sa'an nan a nashi bangaren, mista Cheng Zhimin, wani jami'i mai kula da aikin ilimi a yankin Liangshan, ya ce ilimi zai ba yaran damar samun guraben aikin yi a nan gaba, wanda zai taimaka wajen kau da talauci, da raya tattalin ariziki da zaman al'umma a yankin Liangshan. Zuwa yanzu yawan kananan yaran yankin Liangshan da suka shiga makaranta ya karu zuwa kashi 84.03%, daga kashi 55.40% na shekarar 2015. Ban da wannan kuma an kafa sabbin makarantar kananan yara fiye da 3000 a kauyuka daban daban. A cewar mutanen yankin, wannan nagartaccen matakin da gwamnati ta dauka ya sa su ganin wata makoma mai haske na yankin Liangshan.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China