Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
"Manufofin kasar Sin" sun nuna goyon baya ga ra'ayin cudanyar bangarori da dama
2020-07-29 20:53:36        cri

 

"Kamata ya yi bankin AIIB ya kasance wani sabon dandamali na kasashe mambobinsa, wanda zai inganta samun bunkasuwa tare, da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dan Adam." Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana haka ne a jiya Talata, a yayin taron shekara-shekara ta kafar bidiyo na bankin zuba jarin samar da ababan more rayuwa na Asiya ko AIIB a takaice karo na 5, inda kuma ya gabatar da manufofi guda hudu a fannin, tare kuma da jaddada cewa, za a yi kokarin raya bankin, ta yadda zai kasance wani sabon bankin raya kasa na bangarori da dama, kuma sabon dandamalin gudanarwa dake dacewa da halin da ake ciki, kuma wata sabuwar hukumar hadin kan kasa da kasa bisa babban ma'auni, da kuma sabon misalin koyo na hadin kai tsakanin bangarori da dama na kasa da kasa.

Bisa yanayin da ake ciki na yaki da annobar numfashi ta COVID-19 da tsanantar halin tattalin arzikin duniya, irin manufar da Sin ta dauka, ta nuna tsayayyen goyon baya ga ra'ayin cudanyar bangarori da dama, wadda ta kuma nuna siffar kasar Sin a matsayin wata babbar kasa dake sauke nauyin kanta.

A cikin shekaru hudu da wani abu da suka wuce, yawan kasashe mambobin bankin AIIB ya karu daga 57 a farkon lokacin kafuwarsa zuwa mambobi 102. Ya zuwa yanzu dai bakin ya riga ya zuba jarin kusan dala biliyan 20 a fannin ababen more rayuwa.

Game da manufofi guda hudu da shugaba Xi Jinping ya gabatar, tsohon karamin jakadan kasar Poland dake birnin Shanghai na kasar Sin Sylwester Szafarz ya nuna amincewa sosai gare su. A ganinsa, manufofin za su taimaka wajen warware wasu matsalolin kasa da kasa da ake fuskanta a yanzu, za kuma su samu tsayayyen goyon baya daga wajen dukkan kasashe mambobin bankin, ciki har da kasarsa Poland. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China