Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu mallakar kamfanoni 50 sun yi fice a gasar da gidauniyar Jack Ma ta shirya
2020-07-29 20:32:18        cri
Masu mallakar kamfanoni 50, sun yi fice a zagayen farko na gasar da gidauniyar Jack Ma ta shirya, domin tallafawa masu mallakar kamfanoni a nahiyar Afirka. Bana ce shekara ta biyu, tun bayan fara gudanar da wannan gasa ta shekara shekara mai lakabin "Gwarzayen 'yan kasuwar Afirka ".

Gidauniyar hamshakin dan kasuwar nan na kasar Sin Jack Ma ce ke daukar nauyin wannan gasa.

Mashirya gasar dai sun ce, ana sa ran karrama masu mallakar kamfanoni 100 dake nahiyar cikin shekaru 10, inda za a samar musu da kudin da jimillar su za ta kai dalar Amurka miliyan 100, na tallafi da kuma samar da horon sanin makamar aiki.

A bana, wadanda suka lashe wannan gasa za su samu kyautar kudi da yawan su ya kai dala miliyan 1.5, kana za su samu zarafin shiga rukunin fitattun masu mallakar kamfanoni na kasa da kasa, inda za su ci gajiyar kwarewa, da dabarun kyautata kamfanoninsu, da samun karin horo da albarkatu.

Masu mallakar kamfanoni 50 da suka kai ga nasara a zagayen farko na gasar, sun fito ne daga kasashen Afirka 21, ciki hadda Ghana, da Morocco, da Cote d'Ivoire, da Najeriya, da Masar, da Afirka ta kudu da kuma Kenya. Suna kuma wakiltar sassa 18 na sana'o'i daban daban, ciki hadda fannin noma, da fasahar kwaikwayon tunanin bil Adama, da dabarun tattara manyan bayanai, da hidimomin kasuwanci. Sauran sun hada da fannonin gine gine, da ilimi, akwai kuma mata da yawan su ya kai rabin 'yan takara a gasar ta bana. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China