Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya yi fatan bankin AIIB zai zama wani sabon dandalin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama
2020-07-29 16:20:19        cri

Jiya Talata ne aka kira taron shekara-shekara karo na 5 na bankin zuba jarin samar da ababen more rayuwa na Asiya ko AIIB a takaice ta kafar bidiyo. An kaddamar da ayyukan bankin na AIIB ne a shekarar 2016, bayan da shugaba Xi ya gabatar da shawarar kafuwarsa a shekarar 2013.

A lokacin kafuwarsa, bankin na da mambobi ne 57, amma yanzu yawan mambobinsa ya kai 102, daga nahiyoyi 6 ciki hadda kasashen Asiya, da Turai, da Afirka, da Arewacin Amurka, da kudancin Amurka da kuma Oceania.

A jawabin da ya gabatar yayin taron, shugaba Xi, ya ce yayin da duniya ke kokarin dakile yaduwar annobar numfashi ta COVID-19, dan Adam yana da makoma ta bai daya. Ko shakka babu, ta hanyar nuna goyon baya da hada kai tare ne kawai za a iya warware matsalolin da ake fuskanta, da kara yin hakuri da juna wajen tafiyar da harkokin duniya, da kare tsarin cudanyar bangarori da dama. Kamata ya yi bankin AIIB ya kasance wani sabon dandali tsakanin kasashe mambobinsa, wanda zai inganta samun bunkasuwa tare, da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dan Adam.

Shawarwari guda hudu da Xi ya gabatar kan ci gaban bankin AIIB, su ne na farko, ya kamata a mai da hankali kan batun samun bunkasuwa tare, a kokarin ganin bankin ya zama wani sabon dandali da ke iya ba da gudummawar ci gaban duniya. Na biyu, ya kamata a dukufa kan kirkire-kirkire, a kokarin ganin bankin ya kasance wani sabon dandalin raya duniya da ke tafiya tare da zamani.

Shawara ta uku ita ce, a gudanar da wasu ayyuka masu inaganci, a kokari ganin bankin ya zama wata ingatacciyar sabuwar hukumar hadin kan kasa da kasa da babu kamarta. Shawara ta karshe ita ce, a ci gaba da bude kofa da yin hakuri da juna, a kokarin ganin bankin AIIB ya kasance wani sabon abin koyi ta fuskar hadin kan kasa da kasa. Wannan burin zai ga nasara ne, idan aka martaba ka'idar yin shawarwari da raya ayyuka da more sakamako tare, da dacewa da sauye-sauyen da duniya ke fuskanta, da ma hadin kai tare da karin abokai, a kokarin da ake na dunkulewar tattalin arzikin shiyya-shiyya gu daya, da ma taimakawa duniya wajen samun ci gaba bisa hanyoyin bude kofa ga juna, da hakuri da juna, cin gajiyar juna, samun daidaito, da cimma nasara tare.

Masana daga sassa daban-daban na duniya, sun yaba matuka da shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, suna masu imanin cewa, bankin zai bunkasa ci gaba na bai daya, baya ga zama wani sabon dandalin raya alakar bangarori daban-daban. A cewarsu, hukumomi kamar bankin AIIB na da muhimmanci, musamman ga kasashe masu tasowa, ta yadda za su ci gajiyar bankin wajen kara bunkasa ababan more rayuwarsu, da masana'antu da bangaren aikin gona har ma su samu ci gaba kamar sauran kasashen duniya.

A hannu guda kuma, shigar kasashen na Afirka a dama da su a harkokin bankin, zai ba su damar rage gibin ci gaban dake tsakaninsu da sauran kasashe, sabanin yadda hukumomin kudi irinsu bankin duniya, da IMF ke gindaya tsaurarran sharuddan rance ko ma tallafi ga kasashen kafin su amfana da ko wadanne irin tsare-tsare da suka bullo da su.

A don haka, kafa bankin AIIB tamkar kaya ne ya tsinke a gindin kaba, musamman ga kasashe masu tasowa. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China