Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gani da Ido Maganin Tambaya
2020-07-29 16:10:35        cri

Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, wani bangare ne na kasar Sin mai kunshe da kabilu daban-daban dake zaune cikin zaman lafiya da jituwa. Amma wasu saboda rashin sani ko adawa ko jahiltar abubuwan dake faruwa saboda ba su taba zuwa yankin ba, suke kokarin mayar da fari baki.

Don haka, bai kamata mutane ko kasashe su rika fadin abin da ba su sani ba, don kawai neman biyan bukatunsu na siyasa. Masu azancin magana na cewa, zato zunubi ne, koda ya kasance gaskiya.

Saboda wata manufa ta neman biyan bukata, kwanan baya, kasar Amurka ta sa hannu kan shirin dokar kare hakkin dan Adam ta Uygur na shekara ta 2020, inda ta shafa wa kasar Sin bakin fenti kan yanayin kare hakkin dan Adam da jihar Xinjiang ta kasar Sin ke ciki, da kuma manufofinta na tafiyar da harkokin jihar, lamarin da ya sanya al'ummar Sinawa da ma al'ummar kabilu daban daban na jihar kimanin miliyan 25 yin Allah wadai da nuna adawa da wannan mataki, haka ma al'ummar kasashen duniya masu nuna gaskiya da adalci sun soki matakin na Amurka.

Duk mai bibiyar abubuwan dake faruwa a jihar, ya san cewa, bisa managartan matakan da aka dade ana dauka a jihar Xinjiang, kan yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi a 'yan shekarun da suka gabata, ya sanya jihar shiga cikin sabon zamani na samun wadata da ci gaba.

Yanzu haka an shafe kusan shekaru 3 da wani abu, ba a samu harin ta'addanci a jihar ba. Kuma tun bayan babban taron wakilai na JKS karo na 18, matsakaicin kauwar GDP na jihar ya kai kaso 8.5 cikin 100 a kowace shekara, yawan masu fama da talauci ya ragu daga kashi 19.4 cikin 100 a karshen shekarar 2013 zuwa kashi 1.24 cikin 100 a karshen shekarar 2019.

Yawan wuraren ibada dake jihar Xinjiang ya wuce dubu 28, kuma yawan malaman addini ya kai kusan dubu 30. Kana akwai masallacin dake iya daukar musulmai masu Ibada 530 a lokaci guda 1, adadin da ya zarce na kasashen musulunci masu yawa. Wannan kadai ya ishi mai hankali shaida.

Yanzu haka jihar Xinjiang na cikin wani lokaci mafi kyau na samun wadata da bunkasuwa a tarihi, an tabbatar da 'yancin jama'ar kabilu daban daban dake jihar a fannoni daban daban, ciki har da ikon rayuwa da na samun ci gaba. Shin duk wadannan abubuwan da aka ambata a sama, ci gaba ne ko ci baya? Al'ummar jihar Xinjiang sun fi kowa sanin amsar wannan tambaya. Saboda nasarorin da suka samu.

Daga karshen shekarar 2018 zuwa wannan lokaci, tawagogi sama da 70 da suka kunshi mutane fiye da 1000 da suka fito daga kasashe 91 sun kai ziyara jihar Xinjiang, sun kuma bayyana cewa, abubuwan da suka gani, sun sha bamban da yadda wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka fada. Idan mai fadar magana Wawa ne, ai majiyinta ba Wawa ba ne.

Kokarin da wasu ke yi na yada jita-jita da bata sunan kasar Sin, ba zai goge yanayin ci gaban da jihar ta samu ba. A yayin taron hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD karo na 44 da aka gudanar a kwanakin baya, kasar Belarus ta gabatar da jawabi a madadin kasashe 46, inda suka nuna goyon bayansu kan matakan yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi da Sin take dauka a yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa. Wannan ya nuna cewa, batun Xinjiang batu ne na yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, kuma wanda aka yi dominsa ya sani. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China