Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cin zarafin da Mike Pompeo ya yi wa JKS aikin jahilci ne
2020-07-28 20:21:29        cri

 

Kwanan baya, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ya ba da jawabi a dakin karatu da ajiye kayayyakin tarihi na Richard Nixon, inda ya zargi jam'iyyar dake rike da mulkin kasar Sin wato JKS a takaice, a waje guda kuma ya "yaba wa" jama'ar kasar bisa boyayyiyar manufarta, da nufin tayar da kishi a tsakanin bangarorin biyu, da kuma haifar da sabani da riciki a cikin kasar.

Game da haka, shugaban cibiyar nazarin harkokin waje ta kasar Amurka Richard Haass ya nuna cewa, jawabin da Mike Pompeo ya yi ya nuna cewa, "bai fahimci kasar Sin ba".

Batun ko wata jam'iyyar dake rike da mulkin wata kasa na da kwarewa ko a'a, yana dogaro ne da ko tana iya samun amincewa daga jama'a. A cikin 'yan shekaru a jere da suka wuce, yawan goyon baya da gwamnatin kasar Sin ta samu ya kai matsayin koli, bisa sakamakon binciken da wasu kamfanonin binciken ra'ayin jama'a na duniya. Kaza lika bisa sakamakon binciken da kwararru guda uku na makarantar Harvard Kennedy School suka yi a nan kasar Sin na tsawon shekaru 10 da wani abu, an nuna cewa, Sinawa da yawansu ya wuce kashi 93 cikin 100 sun amince da gwamnatin kasarsu, kuma a ganinsu, dalilin da ya sa jam'iyyar JKS take cike da karfi, shi ne ta samu goyon baya daga wajen jama'a.

A cikin shekaru fiye da 70 da suka wuce da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, jam'iyyar JKS tana jagorancin jama'ar kasar, wajen kafa abun al'ajabi a fannoni masu yawa, har ma kasar ta kasance babbar kasa ta biyu a fannin tattalin arziki a duniya.

 

A yayin da ake tinkarar cutar COVID-19 da ta bulla ba zato ba tsammani kuma, jam'iyyar tana ta tsayawa kan ra'ayin "dora muhimmanci kan jama'a", wannan ne kuma babbar fasahar da kasar ta samu wajen cimma nasarar dakile annobar a cikin watanni uku kacal.

Kamata ya yi Mike Pompeo da mabiyansa su fahimci cewa, matakin "yin zargi kan kasar Sin" ba "Magani ne mai amfani a dukkan fannoni ba" wajen warware matsalolin da kasarsu ke fuskanta. Kana kuma zargin jam'iyyar dake rike da mulkin kasar Sin ma, ba zai boye hasarar da suka yi, wajen rasa amincewa daga wajen jama'ar kasarsu ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China