Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amsa tayin ECOWAS ka iya sulhunta takaddamar siyasar kasar Mali
2020-07-28 16:15:45        cri

Gwamnatin kasar Mali ta amsa kiran kungiyar ECOWAS mai shiga tsakani a rikicin kasar, na kafa gwamnatin hada kan kasa, inda ta sanar da kafa sabuwar majalisar ministoci, wadda aka rage yawansu domin bada damar kafa gwamnatin ta hadaka.

Dumamar yanayin siyasa a kasar Mali na ci gaba da daukar hankalin duniya, inda gammayar 'yan adawa ke kira ga shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita ya yi murabus daga mukaminsa, yayin da masu shiga tsakani ke kira da a kafa gwamnatin hadaka.

Gamayyar kungiyoyin da suka hada da jam'iyyun siyasa da kungiyoyin al'umma da dubban fararen hula, karkashin inuwar "June 5 Movement", na neman shugaban ya sauka ne bisa dogaro da dalilan matasalolin tattalin arziki da tabarbarewar tsaro da suka addabi kasar. Sannan da batun sauya sakamakon zaben kujerun 'yan majalisa 31 da kotun kundin tsarin kasar ta yi, wanda shi ne ya ingiza zanga-zangar.

A farkon watan nan kuma, zanga-zangar ta rikide zuwa rikici tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar, lamarin da ya kai ga sanadin mutuwar mutane 11 da raunatar wasu 150 tsakanin ranar 10 zuwa 12 ga wata, tare kuma da tsare wasu shugabannin 'yan adawar.

An ga irin yadda wadannan rikice-rikice ke daidaita kasashe a nahiyar da gaza cimma burin da aka sanya gaba. Ga misali, har yanzu bayan zanga-zanga da rikice-rikice da asarar rayuka da hambarar da mulki da kafa mulkin hadaka a kasar Sudan, jama'ar kasar na kokawa, duk da cewa ya yi wuri a fara kosawa, tuni al'ummar kasar suka fara kosawa. Wato duk da hatsaniyar da aka fuskanta, kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Duk da cewa kungiyar ECOWAS ta raya yankin yammacin Afrika, ta tura wakilai, ciki har da tawagar shugabannin kasashen kungiyar 5 da suka hada da Ghana da Kwadifwa da Niger da Nigeria da kuma Senegal, da suka yi tattaki zuwa birnin Bamako na Mali a makon da ya gabata, 'yan adawar sun ki amsa kungiyar.

Dukkan bangarorin kasar sun gaza cimma matsaya, domin bangaren adawar sun tsaya kai da fata sai shugaban Ibrahim Boubacar Keita ya yi murabus, wanda ke da kamar wuya. Ba lallai ne a samu biyan dukkan bukatun da ake da su ba, amma ana iya cimma yarjejeniyar da za ta karbu ga kowa. Ya zama wajibi dukkan bangarorin su sadaukar da wasu bukatunsu, idan har kishin kasa da neman ci gabanta ne a zukatansu.

Kamar yadda taron kolin da ECOWAS ta yi jiya dangane da takaddamar ta Mali ta bada shawara, ya kamata a kafa gwamnatin hadin kan kasa da za ta kunshi bangaren adawar da kungiyoyin al'umma, sannan a sake zabukan kujerun 'yan majalisa 31 da ake takkadama kansu, da kuma yiwa kotun kundin tsarin mulkin kasar garambuwul da sako jagoran 'yan adawa da aka sace da kuma gudanar da bincike kan matakin jami'an tsaro da ya kai ga mutuwar wadancan mutane 11.

Duk da cewa zuwa yanzu bangaren adawar ba su ce uffan ba game da shawarwarin, zai fi kyau idan suka yi nazari tare da hawan teburin sulhu maimakon ci gaba da zanga-zanagr dake rikidewa zuwa rikici tare da kai wa ga asarar rayuka. Akwai bukatar tun wuri, a yi wa tukar hanci don gujewa ci gaba da ta'azzarar yanayin. Gazawa wajen shawo kan rikicin na Mali ka iya kara shafar yanayin rashin ingancin tsaro da kasar ke ciki tun 2012, har ma da yankin yammacin nahiyar baki daya.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China