Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Halayyar Amurka na neman yiwa zaman lafiyar duniya barazana
2020-07-27 16:50:25        cri

Masu hikimar magana na cewa, idan zaka gina ramin mugunta to ka gani shi daidai gwabrinka, domin gudun wata rana zaka afka. A karshen makon da ya gabata masanan kasa da kasa sun yi wasu kalaman dake zama a matsayin jirwaye mai kamar wanka game da kalaman rashin dattakun da gwamnatin Amurka ke furtawa kan kasar Sin, inda masanan suka yi gargadin cewa matakin mahukuntan na Amurka yana kara haifar da barazana ga zaman lafiyar duniya, kuma lamarin zai iya zamewa sabon yakin cacar baka kan kasar Sin wanda hakan ya saba wa hakkokin bil adama. Tsokacin kwararrun ya zo ne a lokacin wani taron tattaunawa ta kafar bidiyo mai taken yunkurin kasa da kasa na nuna adawa da sabon yakin cacar baka kan kasar Sin, wanda ya samu halartar kwararru daga kasashen duniya da dama da suka hada da Amurka, Sin, Birtaniya, Indiya, Rasha da Kanada. A ganin masanan, take taken Washingtom ba lallai ne ya haifar wa duniya da mai ido ba. Jenny Clegg, wata kwararriyar malama ce a sashen nazarin al'amurran kasa da kasa a jami'ar Central Lancashire, tace, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tana daya daga cikin dangantaka mafi muhimmanci a tsakanin kasashen duniya, kuma lalacewarta zai iya zama babbar barazana ga zaman lafiyar duniya. Sai dai ba iya Jenny ce kadai ke da irin wannan ra'ayi ba, ita ma Medea Benjamin, wacce ta kafa kungiyar Codepink, wato wata kungiya ce da mata ke jagoranta mai rajin kawo karshen yake-yake a Amurka, tace, ta nuna damuwa matuka bisa ga yadda shugabannin Amurka suke yiwa kasar Sin kage tare da yin ikirarin cewa, wai kasar Sin tana aiwatar da sabbin hanyoyi na tada tsokana, a yayin da kwararriyar ke ganin baiken wadannan kalamai, domin kuwa Amurkar ce kasar da ke kafa sansanonin sojojinta a sassan duniya. To idan kuwa haka ne, wanene ke tada tsokanar?

Magaret Kimberley, wata marubuciyar kafar Black Agenda Report, tace gwamnatin Amurka tana yin mummunan kage kan kasar Sin game da batutuwan dake shafar jahar Xinjiang, da batun yaki da annobar COVID-19, da kuma tilasta rufe karamin ofishin jakadancin Sin dake Houston, matakin da ya saba wa dokokin kasa da kasa. Lallai masu hikimar Magana sun yi gaskiya da suke cewa kifi na ganinka mai jar ko. Hakan ne ya sa wasu kwararrun kasa da kasa suka bukaci bangaren Amurkar da ta kaucewa barazanar tada yakin cacar baka, kana ta nisanci aikata duk wasu abubuwa da ka iya zama mummunar barazana ga zaman lafiyar duniya. Gyara kayan ka dai an ce ba zai taba zama sauke mu raba ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China