Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wata kungiyar mawaka dake cikin kauye
2020-07-27 13:52:52        cri

A nan kasar Sin, wasu manoma sun kafa wata kungiyar rera waka don nishadantar da kansu, tare da nuna farin cikinsu ganin yadda suka samu zaman rayuwa mai inganci.

Kauyen Hongbao yana gundumar Zhongning, dake karkashin garin Zhongwei na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta ta kasar Sin. A cikin kauyen, akwai wata kungiyar masu rera waka da wasu manoma fiye da 80 suka kafa. Dalilin da ya sa wadannan manoma suka kafa kungiyar, shi ne domin nishadantar da kansu, inda suke yin amfani da fasahar rera waka don bayyana muhalli mai kyau na wurinsu, da nuna murnarsu dangane da wani zaman rayuwa mai inganci da ake samu a cikin kauyukan kasar Sin.

An kafa wannan kauye mai suna Hongbao ne ta hanyar kaurar da wasu mutane daga wasu wuraren da ake fama da matsalar muhalli zuwa wannan wuri. Tun daga shekarun 1990, an fara aiwatar da wannan manufa ta kaurar da mutane a jihar Ningxia dake yammacin kasar Sin, don neman fitar da wasu manoma daga kangin talauci. Daga bisani, mutane da yawa sun kaura daga wani yanki mai tsaunuka da ake kira Xi Hai Gu, zuwa wannan kauye. Bisa yin ayyuka cikin himma da kwazo, da manufofin tallafawa matalauta da gwamnatin kasar Sin ta samar, sannu a hankali wadannan mutane sun samu damar kyautata zaman rayuwarsu na yau da kullum, inda karfinsu a fannin tattalin arziki yake ta karuwa, har ma sun shiga cikin wani yanayi na walwala. Sa'an nan bayan da suka samu wani zaman rayuwa mai inganci, mutanen kauyen sun fara nuna sha'awa kan fasahohin al'adu, inda suke neman yin amfani da fasahohin wajen kara dadin zaman rayuwarsu. Saboda haka, zuwa watan Afrilu na shekarar 2019, mutanen kauyen Hongbao sun kafa wannan kuniyar mawaka, bisa samun goyon bayan da jami'an gundumar Zhongning suka bayar.

Mista Li Zhenghong, shi ne shugaban kungiyar, kana daya daga cikin mutanen da ya fara kafa wannan kungiyar mawaka. Ya fadawa wakilinmu cewa, zuwa yanzu, akwai manoma fiye da 80 da suka halarci wannan kungiyar mawaka. Inda matsakaitan shekarunsu sun kai fiye da 40 da haihuwa, kana wasu mutane 4, shekarunsu sun zarce 60 a duniya. Mista Li ya kara da cewa:

"Yawancin su ba su yi karatu sosai ba, har ma wasu fiye da 10 daga cikinsu ba su taba shiga cikin makaranta ba. Duk da haka, sun kwashe fiye da shekara daya suna ta kokarin koyon fasahar rera waka, inda su kan tafi gonaki aiki da rana, sa'an nan suna taruwa a wurin da suke koyon fasahar rera waka karfe 8 na dare a kowace rana, inda suka rera waka har zuwa karfe 11 na dare."

Saboda akwai ayyuka da yawa da rana, don haka wadannan manoma kullum suna gwada fasahar rera wakar ne da dare. A cewar Madam Cao Li, daya daga cikin mambobin kungiyar mawakar, ko da yake ana shan aiki sosai, amma dukkan wadannan manoma suna son rera waka matuka.

"Wani lokaci ana ruwa kamar da bakin kwaya. Duk da haka, idan malaminmu ya ce za a ci gaba da koyon fasahar rera waka, to, dukkanmu za mu zo. A kwanakin nan mutane suna shan aiki sosai a cikin gonakinsu, kullum ba za su iya gama aiki ba har zuwa karfe 8 na dare. Amma bayan da suka gama aiki, nan take zuna zuwa wurin rera wakar, saboda muna jin dadin rera waka matuka. Hakika a kowace rana muna jiran zuwan wannan lokaci na rera waka. Ko da yake mun gaji sosai a wajen aiki, amma muna son zuwa rera waka a kowace rana. Haka ne."

Madam Zhao Cailing, ita ma daya ce daga cikin mambobin kungiyar rera wakar ta kauyen Hongbao. A cewarta shigarta cikin kungiyar nan ta rera waka ta sa ta karu sosai. Da ma saboda tsananin talauci, tana kokarin neman kudin abinci, ba ta da lokacin nishadantarwa. Amma zuwa yanzu ta samu cimma burinta na kyautata zaman rayuwarta, gami da nishadantar da kanta.

"Bayan da na shiga cikin kungiyar rera wakar, to, na ji kamar na samu kwarin gwiwa sosai, inda zan iya saka buri mai kyau game da zaman rayuwata. Na ji dadin sosai, da farin ciki. Yanzu ko a gida ma na kan kara yin magana da mijina da yarana. Hakan ma yana da kyau ga yara."

A ganin mista Li Zhenghong, shugaban kungiyar rera wakar, bayan da aka kafa kungiyar, manoman kauyensu sun kara sanya burika masu kyau game da zaman rayuwarsu. Sa'an nan ta hanyar rera waka tare, sun samar da wani yanayi na hadin gwiwa tare don neman kyautata zaman rayuwa. A cewarsa,

" Mutanen kauyenmu sun canza sosai, bisa rungumar fasahar al'adu ta rera wakoki. Ta wannan hanya, suna nishadantar da kansu, da faranta ransu. Idan an saurari wakokin da muka rera, za a fahimci ci gaban da muka samu, inda muka kawar da talauci, gami da samun zaman rayuwa mai walwala. Muna godiya ga gwamnatinmu, jam'iyya mai mulki wato JKS, kan manufofi masu kyau da suka samar. "

Mutanen kauyen Hongbao sun samu nishadantar da kansu sosai ta hanyar rera waka, bayan da suka samu ci gaban zaman rayuwa. Da fatan, wannan farin ciki nasu zai ci gaba da yaduwa zuwa sauran kauyuka na kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China