2020-07-28 14:33:02 cri |
A zantawarsa da Murtala Zhang, Aminu 1 Naira ya bayyana cewa, ko da yake bai jima da zama a kasar ta Sin ba, amma ya ganema idanunsa babban ci gaban da kasar ta samu a fannoni daban-daban, har ma ya ziyarci wuraren yawon shakatawa da na tarihi da dama a kasar, inda ya ji dadin yadda mutanen kasar Sin ke kulla zumunci da baki 'yan kasashen waje, musamman bakake fata.
Aminu 1 Naira, wanda a yanzu haka yake gudanar da ayyukan gwaji a fannin aikin gona a karkashin jagorancin malaman jami'arsa a lardin Hebei na kasar Sin, ya ce kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen gudanar da aikin gona, ganin yadda take da fasahohi gami da na'urorin zamani masu tarin yawa. Aminu ya kuma bayyana fatansa ga matasan Najeriya don su bada muhimmanci kan ayyukan gona, saboda a cewar malam Bahaushe, noma tushen arziki.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China