Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kyautatuwar tsarin kiwon lafiya ta nuna yadda Sinawa ke cimma burin kafa zaman al'umma mai matsakaicin karfi
2020-07-26 17:34:36        cri

 

Ta dandalin aikin jinya na yanar gizo, masu kamuwa da cutuka dake zaune a wurare masu nisa masu wuyar zuwa suna iya samun jinya daga wajen shahararrun kwararru na asitibocin dake manyan birane na zamani, ta hanyar bidiyo, kuma kwararru suna iya hada kai don ba da jinya ga marasa lafiya, kana da ba su jaroganci kan yadda ake shan magunguna da ba su amsa kan tambayoyin da suka yi musu, ta hanyar yanar gizo kuma asibitocin dake wurare daban daban na kasar Sin suna samar da hidima a fannonin sayen magunguna, biya kudi, jigilar magunguna har ma da gudanar da ayyukan yada ilmin kiwon lafiya ga marasa lafiyar. Yanzu dai, ayyukan bada jinya ta hanyar yanar gizo dake samun saurin ci gaba a nan kasar Sin na kokarin biyan bukatun jama'ar kasar kan kiwon lafiya, tare kuma da kara musu alheri kan zaman rayuwarsu.

Kiwon lafiya bukatu ne na wajibi wajen inganta ci gaban dan Adam a dukkan fannoni, shi ne kuma babban tushe na bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma, wanda ya nuna ko al'umma ta samu wadata da kuma wata kasa ta samu karfi, ko a'a. A waje guda kuma, tabbatar da kiwon lafiyar dukkan al'umma, yana daya daga cikin abubuwan dake cikin burin kafa al'umma mai matsakaicin karfi na kasar Sin.

 

Ta kokarin da aka yi na dogon lokaci, kasar Sin ta riga ta kafa wani cikakken tsarin ba da tabbaci na aikin jinya da ya fi shahara a duniya. Inshorar jinya da kasar ta samar ta shafi yawan al'ummar da ya wuce kashi 95 cikin 100, jama'ar kasar sama da biliyan 1 sun ci gajiya daga tsarin inshorar cututtuka masu tsanani, rukunin da aka fi dora muhimmanci kansa, ciki har da yara da tasoffi da kuma mata masu ciki da ma masu nakuda suna samun babbar hidimar lafiyar jama'a, kana tsarin ba da hidima ga mazauna birane da kauyuka bisa matakai guda uku, hakan ya sa an rage nauyin dake kan jama'a wajen ganin likita. Baya ga haka, adadin kudin da daidaikun mutane ke kashewa wajen samun jinya bisa na jimlar kudin da ake kashewa a fannin ya ragu zuwa matsayi mafi kankanta a cikin shekaru kusan 20 da suka gabata. Ban da wannan kuma, muhimmin ma'aunin kiwon lafiyar jama'a ya fi kyau bisa na matsakaicin matsayin na kasashe matsakaita da mafiya samun kudin shiga a duniya, ana iya cewa, matsayin kiwon lafiyar al'ummar kasar ya karu matuka.

Bisa wannan halin da daukacin duniya ke ciki na yaki da annobar numfashi ta COVID-19, hukumomin kiwon lafiyar kasar Sin suna ta sabunta hanyoyin samar da hidima ga jama'ar kasar ta yanar gizo, matakan da suka kawo alheri ga dukkan jama'ar kasar. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China