Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Saudiyya ta sanar da isar maniyyata aikin hajjin bana na cikin gida
2020-07-26 16:58:38        cri
Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar a ranar Asabar cewa, maniyyata aikin hajjin bana sun isa sabon filin jirgin saman kasa da kasa na sarki Abdulaziz dake Jeddah daga wasu biranen kasar biyar.

A cewar ma'aikatar kula da aikin Hajj ta Umrah ta kasar, alhazan sun fito ne daga biranen Medina, Riyadh, Abha, Tabuk da kuma birnin Jazan, cikin tsauraran matakan kariyar lafiya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudi Press ya bata rahoto.

A yayin da ake tsaka da fuskantar annobar COVID-19, hukumomin kasar Saudiyya sun yanke shawarar takaita adadin mahalarta aikin Hajjin bana zuwa mutanen dake cikin kasar kadai, inda aka dakatar da zuwa maniyyata daga kasashen duniya kimanin 160 wadanda sune kashi 70 bisa 100 da yawan masu halartar aikin Hajjin a duk shekara zuwa kasar mai tsaki.

Har zuwa lokacin kammala aikin Hajjin na bana, za'a cigaba da yin aikin hadin gwiwa tsakanin hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da kare lafiyar mahajjatan, kamar yadda mataimakin sakataren hukumar kula da alhazai na kasar Saudiyya Hussain Al Shareef ya sanar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China