Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin mutanen da suka harbu da COVID-19 a Afrika ya zarce 810,000
2020-07-26 15:54:11        cri
Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Afirka (Africa CDC) ta ce, ya zuwa ranar Asabar, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar Afrika ya kai 810,008.

Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiyar ta kungiyar tarayyar Afrika AU, ta bayyana cikin sabbin alkaluman da ta fitar cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun harbu da COVID-19 ya karu a fadin nahiyar daga 787,501 a ranar Juma'a zuwa 810,008, ya zuwa tsakar ranar Asabar.

Rahoton na Africa CDC ya kara da cewa, adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar cutar ya karu zuwa 17,088 a ranar Asabar, daga adadin mutane 16,697 a ranar Juma'a.

Hukumar dakile yaduwar cutukan ta nahiyar tace, jimillar majinyata 462,374 ne suka warke bayan sun sha fama da cutar ta COVID-19 a Afrika ya zuwa yanzu.

Kasar Afrika ta kudu ce cutar tafi yiwa illa, sai kasashen Masar, Najeriya, Algeria da Morocco, dake bi mata baya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China