Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya yi rangadin aiki a jami'ar koyar da fasahohi da tukin jiragen sama ta rundunar sojin saman kasar Sin
2020-07-24 14:03:38        cri

A gabannin bikin ranar kafa rundunar soja ta kasar Sin dake tafe ranar 1 ga watan Agusta, shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tsakiyar na sojan kasar, ya yi rangadin aiki a jiya Alhamis, a jami'ar koyar da fasahohi da tukin jiragen sama ta rundunar sojin saman kasar, inda ya gaida malamai da daliban jami'ar, da ma dukkan jami'ai da sojojin dake rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasa, da rundunar 'yan sanda masu dauke da makamai, da rukunin dakarun ko ta kwana.

Shugaban ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi a zurfafa yin kwaskwarima, da yin kirkire-kirkire a fannin aikin soja, da kara matsayin koyarwa.

Da kimanin karfe 10 na safiyar ranar 23 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya isa jami'ar koyar da fasahohi da tukin jiragen sama ta rundunar sojin saman kasar Sin dake birnin Changchun na lardin Jilin na kasar.

A dakin nune-nunen jiragen sama na makarantar, Xi Jinping ya binciki ayyukan nune-nune, game da yanayin tunanin asalin jami'ar, wato makarantar jiragen sama ta hadaddiyar rundunar sojan demokuradiyya dake arewa maso gabashin kasar Sin, da yadda ake raya makarantar. Tsohuwar makarantar jiragen saman, makaranta ce dake horar da fasahohi, da tukin jiragen sama ta farko, da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kafa. Hadin kai, da raya sana'a, da bautawa, da kuma habaka sabuwar hanya, sun kasance tunani na tsohuwar makarantar. Xi Jinping ya ba da shawarar ci gaba da tunawa da tarihi, da kuma kara raya tunanin tsohuwar makarantar.

Daga baya kuma, ya isa wurin horas da sojoji, inda ya yi mu'amala tare da dalibai.

"Daliba: Sannu shugaba, ni ce Zhou Yixuan, ina koyon tukin jirgin saman.

Xi Jinping: Shekarunki na haihuwa nawa?

Daliba: An haife ni a shekarar 2001, shekarun haihuwa ta 19.

Xi Jinping: Dukkanku kun kammala karatu a makarantar sakandare ko? Bayan horo da kuma jarrabawar da aka yi muku, babu lokaci mai yawa. Ya kamata ku yi amfani da wannan dama, mu ma kamata ya yi mu kiyaye ku. Dukkanku fata ne na jam'iyya da jama'a, ku ma za ku cimma burin kasarmu na karfafa aikin soja a nan gaba."

Bayan haka kuma, Xi Jinping ya kara wa daliban kwarin gwiwa, na kara kokari kan karatu da horo, don kasancewa kwararru tun da wuri, wanda hakan zai sa su taka rawar gani kan karfafa karfin soja.

"Babu rundunar soja mai karfi, babu kasa mai karfi. Ana samun rundunar soja mai karfi ne bisa matakai daya bayan daya. Tun daga makarantar soja, dole ne mu habaka kyakkyawan yanayin gargajiya, da tunanin jarumai. Ban da jiragen sama da makaman kiyaye tsaron sararin sama na zamani, muna kuma bukatar jaruntaka irin ta rashin tsoron dukkan makiya masu karfi. Wannan ne tunaninmu na kara karfin soja, ina fata za ku kara kokari don samun maki mai kyau."

Bayan haka kuma, Xi Jinping ya iso dakin gwaji na jirgin sama marasa matuki, don binciken na'urorin koyar da fasahohin tukin jirgin saman, da fahimtar yadda ake hoyar da matukin jirgin saman. Xi Jinping ya ce, yanzu an bullo da yawan tsarin jirgin sama marasa matuka iri daban daban, amfani da jirgin saman marasa matuki wajen yaki yana ta canja halin yake-yake. Don haka, ya kamata a kara yin nazari kan yake-yake ta hanyar jirgin sama marasa matuki, da raya sana'ar, da kara horar da kwararru a fannin.

Bayan ya saurari rahoton ayyuka na makarantar, Xi Jinping ya ba da jawabi cewa, kamata ya yi a saba da sabon halin da ake ciki, da sabon nauyin dake bisa wuya, da tabbatar da burin da ake fatan cimmawa wajen ba da horo, kana da kara yin shiri na dogon lokaci, da mayar da tsare-tsaren kara karfin soja ta hanyar horar da kwararru, a matsayin wani shirin ci gaba da hakikanin matakan da za a dauka, za kuma a tabbatar da haka a dukkan fannonin da suka shafi harkokin jami'ar. Baya ga haka, ya kamata a fahimci halin musamman na girman kwararru, don kyautata tsarin ba da horo, da kuma kara ingancin kwararru.

A cikin jawabinsa kuma, Xi Jinping ya nuna cewa, akwai bukatar hada kan makaranta da rundunar sosai, da kara kyautata halin kwasa-kwasai, da halin wuraren yaki sosai, ta haka za a iya horar da kwararrun da ake bukata.

Dadin dadawa, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a dora muhimmanci kan kyautata tsarin jiragen sama, a kuma kara kokari kan fannonin sauyawar tunani, da horar da kwararru, da nazari kan manufofin aikin soja, da yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha kan tsaron kasa da dai sauransu.

A karshe dai, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a gudanar da ayyukan dakile yaduwar annobar COVID-19 da ake fuskanta, bisa wannan tushe ne ake gudanar da ayyuka daban daban, kana da kara daukar matakai don cimma burin da aka tsara. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China