Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai dace zargi da kin jini su gurgunta alakar Sin da Amurka ba in ji Cui Tiankai
2020-07-20 12:03:10        cri

Jakadan Sin a Amurka Cui Tiankai, ya ce gano hanyoyin cimma matsaya daya tsakanin Sin da Amurka, na cikin dabarun kara inganta alakar sassan biyu, da kuma warware sabani dake tsakanin su. Kuma bai kamata a kyale zargi, da tsoro ko kin jini, su gurgunta kyakkyawar huldar waje dake tsakanin sassan ba.

Cui Tiankai ya kara da cewa "A wurin mu, shugaba Trump shugaba ne na Amurka da Amurkawa suka zaba, don haka a shirye muke mu yi aiki tare da shi da gwamnatin sa, wajen gina tsari mai cike da daidaito, da alaka mai karfi tsakanin kasashen nan namu manya guda biyu.

Cui ya yi wannan tsokaci ne, yayin wata zantawa a jiya Lahadi da wakilin kafar CNN Fareed Zakaria. Ya ce ko shakka shugabannin Amurka, da ma ko wacce gwamnati dake mulkin kasar, za su kare muradun kasar, kuma haka ma abun yake a bangaren gwamnatin Sin.

Jami'in diflomasiyyar na amsa wata tambaya ne game da alakar gwamnatocin Sin da Amurka, inda ya ce abun lura shi ne karuwar fannonin da sassan biyu ke da buri iri daya, da fannonin da suke da damar yin aiki tare don cimma moriyar al'ummun su, da manyan burikan bai daya na al'ummun kasa da kasa.

A hannu guda kuma, akwai bukatar mu yi kyakkyawan aikin rage banbance banbance tsakanin mu ta hanyoyi mafiya dacewa. Wannan a cewar jami'in, tun tuni su ne matakan da Sin ke aiwatarwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China