Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta samar wa kauyuka fasahohin sadarwa na zamani don bunkasa yankunan karkara
2020-07-20 10:15:43        cri
Mahukuntan kasar Sin, sun fitar da wata takardar sanarwa mai nasaba da ayyukan gwaji, na bunkasa fannin fasahar sadarwa ta zamani a yankunan karkarar kasar.

Takardar wadda sassan hukumomi masu ruwa da tsaki 7 na kasar suka fitar cikin hadin gwiwa, ciki hadda hukumar lura da harkokin yanar gizo, da ma'aikatar ayyukan noma da raya karkara, da hukumar bunkasa samar da ci gaba da gudanar da sauye sauye.

Takardar ta ce shirin ya kunshi dukkanin tsari da yanayin gudanarwar kauyen na fasahar sadarwa, da dabarun cin gajiya daga fasahohin sadarwa da kauyukan da za su shiga shirin za su amfana da su. Kauyukan za su mori sabbin dabarun raya tattalin arziki, da na gudanarwa a karkara, da dai sauran su.

Shirin na gwaji, na da nufin rage gibin dake tsakanin birane da kauyuka ta fuskar cin gajiyar fasahohin zamani, da fadada ci gaban fasahohin tattalin arziki na zamani nan da karshen shekara ta 2021.

Kaza lika karkashin wannan shiri, za a bunkasa shigar da manyan wayoyin samar da yanar gizo, da na wayoyin salula, da kafofin talabijin na zamani, da kafofin intenet da ake yayi a duniya a sassan yankunan karkara. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China