Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan siyasar Amurka dake sukar JKS suna shafawa kansu bakin fenti
2020-07-18 16:53:02        cri

A kwanakin baya bayan nan wasu 'yan siyasar Amurka, kamar su sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo da mataimakin sakataren harkokin tsaron kasar Robert C.Obrien, suna ta sukar jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin, domin lalata huldar dake tsakanin jam'iyyar da al'ummun kasar. Amma a farkon watan Yulin da muke ciki, wani rahoton da jami'ar Harvard ta fitar bayan ta shafe shekaru 14 tana nazari, ya nuna cewa, al'ummun kasar Sin suna gamsuwa matuka da ayyukan gwamnatin kasar, har alkaluman gamsuwar sun kai sama da kaso 90 bisa dari, sakamakon da ya nuna cewa, al'ummun kasar suna goyon bayan JKS sosai, kana ya shaida cewa, wadancan 'yan siyasar, suna shafawa kansu bakin fenti.

Hakika yunkurinsu shi ne haifar da kiyayya tsakanin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da al'ummun Sinawa, tare kuma da hana ci gaban kasar ta Sin, kana suna son dora laifi kan kasar Sin, kasancewar gwamnatin Amurka ba ta yi nasara wajen hana yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ba.

Bisa matsayinta na babbar jam'iyya mai tsawon tarihin sama da shekaru kusan 100, tun farkon kafuwarta, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana sanya moriyar al'ummun kasar gaba da komai, a sanadin haka ta samu goyon baya daga al'ummun Sinawa matuka, alal misali, yayin da kasar Sin take fuskantar annobar COVID-19, gwamnatin kasar ta yi kokari gwargwadon karfi karkashin jagorancin JKS domin ceton rayukan al'ummun kasar, inda ta biya daukacin kudin da ake bukata domin jinyar wadanda suka kamu da cutar.

Amma a kasar Amurka, an lura cewa, 'yan siyasar kasar sun fi ba da muhimmanci kan moriyar siyasa da kudin da ake kashewa, da kuma kuri'un da za a kada, har ta kai su ga asarar muhimmin lokacin hana yaduwar annobar.

Dalilin da ya sa kasashen Sin da Amurka suka shiga yanayi mabanbanta yayin da suke dakile annobar shi ne, a kasar Sin, moriyar jam'iyyar kwaminis mai mulki ta yi daidai da ta al'ummun kasar, amma a Amurka, gwamnatin kasar tana samar da hidima ne ga wasu manyan rukunoni, a maimakon daukacin al'ummun kasar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China