Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan cinikin waje da ake yi tsakanin Sin da ketare ta yanar gizo na karuwa sosai
2020-07-17 12:45:06        cri

A cikin farkon rabin shekarar bana, yawan cinikin shige da fice ta yanar gizo da aka yi tsakanin kasar Sin da ketare ya karu fiye da kashi goma da wani abu. A yayin da ake kokarin dakile yaduwar annobar COVID-19 a duk fadin duniya, cinikin waje ta yanar gizo tsakanin kasa da kasa ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da karuwar cinikin waje. Masu sharhi na ganin cewa, tabbas yin cinikin waje ta yanar gizo tsakanin kasa da kasa zai ci gaba da karuwa a shekarar da muke ciki, kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa cinikayya tsakanin kasa da kasa.

A kwanan baya, dakin adana kayayyaki na kamfanin sayayya ta shafin intanet na Lazada, wato shafin intanet na sayayya mafi girma a yankin kudu maso gabashin Asiya, ya inganta fasahohinsa na rarraba kayayyaki. Sakamakon haka, yawan kayayyakin da ake saya daga shafin ya karu sosai. Madam Qiuyue, wadda ke kula da harkokin kamfanin Lazada ta ce, kamfaninta ya ci gajiyar wata sabuwar manufar da babbar kwastan ta kasar Sin take gwadawa a wasu hukumomin kwastam dake biranen Beijing da Tianjin da Nanjing na kasar Sin domin kara bunkasa cinikin waje ta yanar gizo. Madam Qiuyue ta ce, "Salon rarraba kayayyaki a dakin adana kayayyakinmu dake ketare shi ne, idan mai sayar da kayayyaki ya isar da kayayyakin a cikin irin wadannan daki, duk wanda ya sayi wadannan kayayyaki a ketare zai iya samun kayansa kamar yadda ya saba saya a kasar da yake zaune. Sakamakon haka, dukkan masu sayayya na ketare za su iya sayen kayayyaki cikin sauki. Yanzu babbar hukumar kwastan ta kasar Sin tana gwada wannan sabuwar manufa ta B2B a irin wadannan dakunan rarraba kayayyakin kamfanin dake ketare. Yanzu, dakin rarraba kayayyaki na kamfanin Lazada ya kara saurin rarraba kayayyaki sakamakon wannan manufa. Kamfanonin kanana ko matsakaita na kasar Sin za su iya rage tsawon lokaci daga kwanaki biyu zuwa wasu dakika kadai wajen daidaita harkokin kwastan."

"Sabuwar manufar kwastan" wato manufar B2B da madam Qiuyue ta kamfanin Lazada ta ambata ita ce, matakin da babbar hukumar kwastan ta kasar Sin take gwadawa a wasu kananan hukumomin kwastan dake sassa daban daban na kasar Sin. Bisa wannan mataki, ana sa ido kan yadda ake mayar da kayayyakin da aka saya ta yanar gizo a ketare daga kanana ko matsakaita na kamfanonin kasar Sin domin kokarin ingiza kamfanonin shige da fice na kasar Sin da su sayar da kayayyakinsu a duk fadin duniya ta yanar gizo a yayin da ake tinkarar annobar COVID-19 a duk fadin duniya.

Mr. Li Kuiwen, kakakin babbar hukumar kwastan ta kasar Sin ya bayyana wa kafofin watsa labaru a kwanan baya a nan Beijing, cewar wannan matakin da ake gwadawa zai taimakawa kanana da matsakaitan kamfanoni wajen daidaita harkokin kwastan. Li Kuiwen yana ganin cewa, "Yanzu muna gwada aiwatar da sabuwar manufar B2B a kananan hukumomin kwastan 10 dake biranen Beijing da Tianjin da Nanjing da Hangzhou da Shenzhen da Ningbo da dai sauransu. Sakamakon haka, yanzu mun shiga sabuwar hanyar sayar da kayayyaki a duk fadin duniya ta yanar gizo. Dukkan kamfanoni wadanda suke aiwatar da wannan sabuwar manufa za su iya yin rajista sau daya, da saukaka matakan neman izinin fitar da kayansu da makamatansu. Wasu kananan kamfanoni za su iya zabar wasu dabaru mafi dacewa a lokacin da suke fitar da kayayyaki marasa dajara. Za a iya kuma cin moriyar wannan sabuwar manufa a lokacin da ake fitar da kayayyakin da masu sayayya suka saya a yayin bikin baje koli na Guangzhou da aka shirya ta yanar gizo."

Sabbin alkaluma da babbar hukumar kwastan ta kasar Sin ta fitar, sun nuna cewa, a watanni shida na farkon bana, yawan kayayyakin da aka saya ta yanar gizo kuma aka kuma fitar da su zuwa ketare ya karu da 28.7%, sannan yawan kayayyakin da aka sayo daga ketare ta yanar gizo ya karu da 24.4%. Wadannan alkaluma sun wuce saurin karuwar gaba dayan cinikin waje da kasar Sin ta yi a cikin wadannan watanni shida na farkon shekarar bana.

Game da wannan sabuwar manufa, Mr. Hu Qimu, mai zanarin tattalin arzikin yanar gizo a nan kasar Sin yana ganin cewa, nan da wani lokaci mai zuwa a bana, kamfanonin cinikin waje ta yanar gizo za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen fitar da karin kayayyaki zuwa ketare. A cewar Hu Qimu, "Wasu kamfanonin cinikin waje ta yanar gizo za su iya yin amfani da bayanan yanar gizo a shafinsu na intanet, ta yadda za su iya sanin abubuwan da ake bukata a kasuwannin ketare. Sakamakon haka, za a fitar ko shigo da karin kayayyaki ta yanar gizo." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China