Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
KO YA DACE TOKYO TA KARBI BAKUNCIN GASAR OLYMPICS DAKE TAFE
2020-07-16 14:55:00        cri

Ra'ayin 'yan takarar kujerar gwamna a jihar Tokyo ta kasar Japan, ya sha banban game da dacewar gudanar da gasar Olympics da aka shirya gudanarwa a birnin, a gabar da ake daf da tabbatar da wanda ya lashe kuri'un zaben gwamnan jihar nan ba da jimawa ba.

'Yan takarar gwamnan Tokyo na ci gaba da bayyana mahangar su game da wannan batu, inda gwamnar jihar mai ci yuriko Koike, ke ganin dacewar ci gaba da shirin karbar wannan gasa bisa lokacin da aka tsara, yayin da wasu daga sauran 'yan takarar gwamna a jihar ke sukar hakan.

Koike dai na ganin akwai yiwuwar shawo kan kalubalen cutar COVID-19 a Tokyo, ta yadda za akai ga gudanar da gasar ta Olympics lami lafi, a lokacin zafi dake tafe kamar yadda aka tsara. Sai dai a cewar ta, ya kamata a saukaka tsarin wasan ta yadda za a rage adadin kudaden da za a kashe yayin gudanar sa.

A daya bangaren kuma, daya daga 'yan takarar, wanda kuma a baya ya kasance dan takarar mataimakin gwamnan yankin Kumamoto Mr. Taisuke Ono, na ganin abu mafi dacewa shi ne dage gasar zuwa shekarar 2022 ko 2024, domin tabbatar da ganin bayan wannan cuta gaba daya. Wannan ra'ayi na sa ya yi daidai da na Takashi Tachibana, wanda shi ma ke ganin dacewar dage gudanar da gasar.

Shi kuwa dan takara Yasutaro Yamamoto, wanda jarumin fina finai ne da a yanzu ya shiga jerin 'yan takara, na da ra'ayin soke gudanar da gasar ne gaba daya. Yamamoto na ganin tunda dai cutar ba ta da magani, kuma tana kara kamari a kasashen duniya masu yawa, kamata ya yi a yi hakuri a soke gudanar da ita.

Shi ma dan takara Utsunomiya mai shekaru 73 a duniya, wanda kuma lauya ne da a yanzu ke takarar kujerar gwamnan birnin Tokyo a karo na 4, yana ganin a soke gasar kawai. Utsunomiya tsohon shugaban kungiyar lauyoyin kasar ya ce hakan ya fi dacewa, duba da kalubalen da jami'an lafiya za su fuskanta, idan aka dage sai an gudanar da gasar a shekara mai zuwa.

A hannu guda kuma, wasu alkaluma na sakamakon karshe, game da wani binciken jin ra'ayin jama'ar birnin sun nuna cewa, sama da kaso 50 bisa dari na mazauna birnin Tokyo, na da ra'ayin ko dai a dage gasar ko kuma a soke ta gaba daya. Rahotanni sun ce kaso 27.7 bisa dari na al'ummar birnin na kira da a soke gasar, yayin da kaso 24 bisa dari ke cewa zai fi dacewa a sake dage ta.

A bangaren farin jinin 'yan takarar kujerar gwamnan birnin kuwa, alkaluman jin ra'ayin jama'a sun nuna cewa, gwamna mai ci Koike ce ke kan gaba, idan ta dara sauran 'yan takara sama da 21 farin jini wurin masu kada kuri'ar zaben, wanda za a kidaya kuri'unsa ranar 5 ga watan nan.

ZA A CI GABA DA KEWAYE DA WUTAR GASAR OLYMPIC TA TOKYO DAGA RAN 25 GA WATAN MARIS NA SHEKARA MAI ZUWA

Wata kafar watsa labarai ta kasar Japan, ta rawaito mashirya gasar Olympic ta birnin Tokyo na cewa, za a ci gaba da kewaye da ake yi da wutar Yula ta gasar Tokyon tun daga ranar 25 ga watan Maris na shekara mai zuwa. Matakin ya biyo bayan dage gasar da aka yi da shekara guda, sakamakon bazuwar cutar COVID-19 a sassan duniya, don haka aka dakatar da kewayawa da wutar, wadda ke alamta shirye shiryen bude gasar.

An ce dakatar da kewayawa da wutar na cikin matakan kara saukaka shirye shiryen fara gasar da aka tsara gudanarwa, kuma da zarar an ci gaba da kewayen, za a kwashe kwanaki 121 ana yin sa, bisa kuma hanyoyin da aka saba bi tare da wutar ta wannan gasa.

Bayan sauya lokacin, an tsara kewaye da wutar gasar ne tun daga kauyen Fukushima, zuwa wasu yankuna 47 da birane 859 cikin kwanaki 121, kafin kuma daga bisani a bude gasar a sabon filin wasa na kasar ranar 23 ga watan Yuli. A baya kuwa, an tsara gudanar da kewayen ne daga ranar 26 ga watan Maris na bana, amma bayan dage gasar, sai aka kuma dage fara kewayen da kwana guda.

Da yake tsokaci kan hakan, mataimakin babban sakataren shirya gasar Yukihiko Nunomura, ya ce manufar su a yanzu ita ce aiwatar da dukkanin matakan kara saukaka kewaye da fitilar, tare da wanzar da yawan 'yan wasa 10,000 da za su shiga a dama da su, baya ga kiyaye wuraren da za ta gudana.

Duk da cewa an gabatar da hanyoyin rage tsayin lokacin kewayen, har yanzu akwai yiwuwar karuwar tsadar gudanar da ita. Bayan duba na tsanaki game da hanyoyin da za a bi, an gano cewa, yadda aka tsara a baya shi ne mafi dacewa.

Mahukuntan gasar sun tabbatar da cewa, za a bi tsarin kewayen yadda ya kamata, amma za a ci gaba da aiwatar da dabarun saukaka bikin isar wutar gasar zuwa filin da za a kaddamar da wasan. Kaza lika kananan hukumomi na da hurumin tsara kaucewa cunkoson jama'a, yayin da ake ratsawa da wutar zuwa sassa daban daban, domin kaucewa sake bullar cutar COVID-19 a wuraren da ta riga ta yi sauki.

Arsenal ba ta motsa a matakinta a teburin Premier ba

Sa'o'i 3 da suka wuce

Mai tsaron ragar Leicester Ciry, Kasper Schmeichel ya hana Arsenal ta kara zura masa kwallo, inda ya tare damar da Alexandre Lacazette da ta Bukayo Saka da suka samu.

Arsenal ta koma buga karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Eddie Nketiah jan kati saura minti 15 a tashi daga fafatawar.

An kori Nketiah wanda ya canji dan wasa minti hudu da shiga fili, bisa ketar da ya yi wa James Justin.

Leicester ta farke kwallo ta hannun Vardy, bayan da Demaray Gray ya buga kwallo ta je wajensa saura minti hudu a tashi wasa.

Sai da alkalin wasa ya tuntubi na'urar da ke taimaka masa yanke hukunci wato VAR wacce ta ce Vardy bai yi satar gida ba.

Vardy ya ci kwallo 22 kenan a gasar Premier League ta shekarar nan da tazarar guda biyu tsakaninsa da dan wasan Arsenal, Aubameyang mai 20 a raga.

Da wannan sakamakon Gunners ta samu karin maki daya tal, amma tana nan a matakinta na bakwai a teburi da take fatan samun gurbin buga gasar zakarun Turai ta badi.

Ita kuwa Leicester City ta yi kasa zuwa mataki na hudu, bayan da Chelsea ta maye gurbinta, sakamakon doke Crystal Palace 3-2 da ta yi a ranar Talata.

'Yan Barcelona da za su fafata da Espanyol a La Liga

Barcelona ta ci kwallayenta ta hannun Luis Suarez da kuma Arturo Vidal, yayin da David Lopez da kuma Wu Lei na Espanyol suka zura kwallo a ragar Barca.

Tun a sanyin safiyar Talata, Barcelona ta yi atisayen karbar bakuncin Espanyol, sannan ta bayyana wadanda za su buga mata karawar.

Kuma dukkan 'yan kwallon Barca sun halarci atisayen har da Frenkie de Jong, yayin da Junior ya motsa jiki shi kadai ba cikin 'yan wasa ba.

Dan wasan mai tsaron baya na fama da ciwon kugu, kuma ba zai buga karawa da Espanyol ba, za kuma ta auna koshin lafiyarsa nan gaba.

A ranar Lahadi Barcelona ta je ta doke Villareal 4-1, hakan ne ya bai wa kungiyar rage tazarar maki tsakaninta da Real Madrid ya koma hudu kawo yanzu.

Kocin Barcelona ya bayyana 'yan wasa 23 da za su fafata da Espanyol. bai yi canji ba daga wadanda suka doke Villareal a ranar Lahadi ba.

'Yan kwallon Barcelona da za su fuskanci Espanyol:

Ter Stegen da N. Semedo da Piqué da I. Rakitic da Sergio da Arthur da Suárez da Messi da Neto da Lenglet da Griezmann da Jordi Alba da Braithwaite da kuma S. Roberto.

Sauran 'yan wasan sun hada da, Vidal da Iñaki Peña da Riqui Puig da Collado da Ansu Fati da R. Araujo da Morer da Monchu i J da kuma Cuenca.

Wadanda ke jinya sun hada Queden da Dembélé da De Jong da Umtiti da kuma Junior.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China