Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An farfado da aikin layin dogo na Madaraka a Kenya
2020-07-16 14:51:05        cri

Layin dogo na Madaraka a Kenya daya ne daga cikin wasu manyan ababen more rayuwa da Sin ta taimaka wajen gina wa a nahiyar Afrika. Ran 13 ga wata, aka dawo da wannan aiki, bayan dakatar da shi a tsawon watanni uku saboda bullar cutar COVID-19.

Da misali karfe 8 na safiyar ranar 13 ga wata, jirgin kasa dauke da fasinjoji 482 ya fara aiki a kan layi dogon na Madaraka wato layin da ya hada birane Mombasa da Nairobi, bayan dakatar da aiki na kwanaki 97

A sakamakon barkewar cutar COVID-19, gwamnatin kasar Kenya ta sanar da killace wadannan birane biyu, hakan ya sa jiragen kasan jigilar fasinjoji sun daina ayyuka daga ran 7 ga watan Afrilu. Bayan sake farfado da harkokin rayuwa da na tattalin arziki a kasar, layin dogo ya dawo aiki a ran 13 ga wata. Saboda yadda ake ci gaba da aiwatar da dokar hana fitar dare a Kenya, ya sa an kyautata jadawalin zirga-zirgar jirgin, wato kai da dawo sau daya a ko wace rana. Ban da wannan kuma, an sayar da rabin tikiti don tabbatar da tsarin nan na ba da tazara. Manajan gudanarwar kamfanin layin dogo na African Star, Li Jiuping ya ce:

"Mun yi shirin tsaf bisa bukatun gwamnatin dangane da aikin kandagarki, alal misali, binciken yanayin zafin fasinjoji da suka shiga tashar da fesa maganin kashe kwayoyin cuta a kujeru dake cikin dakin jiran jirgi da kiyaye tazarar dake tsakanin fasinjoji yayin da ake layin jiran jirgi da kaucewa cunkuso. Ban da wannan kuma, ana ba da tazarar kujera a tsakanin fasinjoji yayin da ake sayar da tikiti. Mun kuma kebe wani taragu don killace wadanda ake zaton suna dauke da cutar. Saboda wannan tsari da muke dauka, an sayar da dukkan tikiti na yau da kuma gobe cikin gajeren lokaci."

Ya zuwa yanzu, an sanar da cewa, mutane fiye da dubu 10 sun kamu da cutar Covid-19 a kasar ta Kenya, kuma 80% daga cikinsu, ba su nuna alamun kamuwa da cutar ba. A game da wannan, Li Jiuping ya bayyana cewa:

"Ko da yake muna bincike yanayin zafin jikin fasinjoji, amma hakan ba zai sa a gano wadanda suka kamu da cutar ba tare da nuna alama ba. Hakan ya sa, muke horar da ma'aikantanmu, da bukatar su sanya marufin baki da hanci da rigar kandagarki da tabarau da kuma safar hannu, baya ga kayayyakin kashe kwayoyin cutar da muke samarwa a cikin jirgin."

Ko da yake a baya an dakatar da aikin jigilar fasinjoji a kan wannan layi, amma jiragen dakon kayayyakin jiyya sun yi ta zirga-zirga a kan layin, matakin da ya ba da babbar gudunmawa wajen taimakawa kasar yakar cutar. Ya zuwa ran 30 ga watan Yuni, an yi jigilar kwantenoni dubu 196, ciki hadda abinci iri-iri da kayayyakin kandagarki da dai sauransu. Rahotanni na cewa, a watan Yuni, yawan jiragen kasa da suka zirga-zirga a kan wannan layi tsakanin Nairobi fadar mulkin kasar da Mombasa dake dab da teku, ya kai 14 a ko wace rana, yawan kwantenoni da aka yi jigilar su ya kai 34688, nauyinsu ya kai ton 382227. A sa'i daya kuma, gwamnatin Kenya ta fara amfani da tashar Naivasha don ta zama tashar canja jirgi mafi muhimmanci a gabashin Afrika a lokacin cutar, don hana yaduwar cutar zuwa gabashin Afrika.

Mataimakiyar manajan sashin al'adun gudanarwar kamfanin African Star Olivia Mengichi ta ce:

"Ya zuwa ran 30 ga watan Yuni na wannan shekara, mun yi jigilar kayayyakin kandagarki har ton 806, alal misali magungunan kashe kwayar cutar da dai sauransu. Gwamnatin ta hana zirga-zirgar mutane a arewacin kasar, saboda haka mun yi amfani da wannan layi don jigilar kayayyaki zuwa tashar Naivasha, don rage zirga-zirgar manyan motocin daukan kayayyaki, hakan zai ba da gudunmawa wajen hana yaduwar cutar a tsakanin al'ummar wurin."

Kazalika, kamfanin ya ce, sake amfani da wannan layi ya saukakawa mazauna yin tafiye-tafiye da hana yaduwar cutar ta hanyoyin mota don sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin kasar lokacin da ake tsaka da fama da cutar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China