Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude kamfanin raya ayyukan da ba sa gurbata muhalli a Shanghai
2020-07-16 11:19:59        cri

A jiya ne aka bude wani kamfani, dake aikin tattara kudaden gudanar da ayyuka marasa gurbata muhalli a birnin Shanghai na kasar Sin, da jarin da ya kai Yuan biliyan 88.5, kwatankwacin dala biliyan 12.66.

Ma'aikatar kudi da ta muhallin halittu da kare muhalli da gwamnatin birnin Shanghai ne suka kaddamar da kamfanin mai suna National Green development Fund a turance.

Za a yi amfani da kudaden da kamfani ya tara, wajen zuba jari a fannoni kamar su, kare gurbatar muhalli, kare lalacewar muhallin halittu, da dasa itatuwa a filayen kasa, kare makamashi da albarkatu, harkokin sufuri maras gurbata muhalli da makamashi mai tsafta.

A jawabinsa shugaban rukunin kamfanin Chen Yin, ya ce kamfanin ya tsara kimanin ayyuka daban-daban guda 80 wadanda ba sa gurbata muhalli.

Asusun da aka kafa, wanda zai mayar da hankali kan muhimman sassa da ba sa gurbata muhalli a zirin tattalin arziki na Kogin Yangtze, zai fito da sabbin hanyoyi don dorawa kan ci gaban da aka samu a fannin raya muhallin halittu na kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China