Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Aikin "diflomasiyya ta kafar bidiyo" da shugaban kasar Sin ya yi ya kara imanin kasa da kasa
2020-07-15 11:25:20        cri

Bana, cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar da kalubaloli iri daban daban ga kasashen duniya. A wannan lokacin da duniya ke fuskantar sauye-sauye, kasar Sin ta dukufa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya. A watanni shida na farkon shekarar bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci manyan tarukan kasa da kasa guda uku ta kafar bidiyo, inda ya kuma gabatar da jawabai. Sa'an nan, ya kuma aika wasiku sama da 20 da amsa wasikun da 'yan kasar Sin da na ketare suka rubuto masa. Ban da haka kuma, ya yi hira ta wayar tarho sau 60 da jami'an kasashen waje da wakilan kungiyoyin kasa da kasa game da batutuwan yin kandagarki da dakile yaduwar cututtuka.

Bugu da kari, ya yi musayar ra'ayoyi da bangarori daban daban dangane da fasahohin yaki da annoba, da yin kira ga kasa da kasa wajen karfafa hadin gwiwarsu ta fuskar farfado da tattalin arziki, da inganta dunkulewar al'ummomin kasa da kasa a fannin kiwon lafiya.

Ta hanyar "diflomsiyya ta kafar bidiyo", shugaba Xi Jinping ya jagoranci kasar Sin, ta yadda za ta kasance muhimmin bangaren yaki da cutar COVID-19 a duk fadin duniya, da kuma muhimmiyar kasa dake kare zaman lafiya da ci gaban kasa da kasa.

A yayin taron kolin shugabannin kungiyar G20 da aka yi a ranar 26 ga watan Maris, shugaba Xi ya sanar da cewa, Sin za ta yi hadin gwiwa da kasashen duniya wajen yin musayar ra'ayoyi kan fasahohin yaki da cutar, da nazarin magunguna da allurar rigakafi, kana za ta tattauna da kasashen duniya wajen bullo da tsarin fuskantar harkokin kiwon lafiya na gaggawa, da samar wa kasuwannin duniya karin magunguna, da kayayyakin yau da kullum, da na kandagarki da dakile yaduwar cututtuka da sauransu.

Babu wata kasa da za ta yi nasarar yaki da cutar ita kadai, dole ne mu hada kanmu don yaki da cutar, ta yadda za mu cimma nasara, da farfado da tattalin arziki.

Kana a yayin taron kolin G20, Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taken "Ya kamata mu hada kai, domin cimma nasara", sa'an nan, a bikin bude babban taron kiwon lafiya na kasa da kasa karo na 73, ya gabatar da jawabi mai taken "Yin hadin gwiwa domin cimma nasarar yaki da cutar COVID-19, da karfafa dunkulewar al'ummomin kasa da kasa ta fuskar kiwon lafiya", kana, a taron kolin hadin gwiwar Sin da Afirka kan yaki da cutar COVID-19, ya gabatar da jawabi mai taken "Hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19, domin cimma nasara tare", cikin wadannan jawabai da ya gabatar, ya mai da hankali matuka a fannin yin hadin gwiwa.

Yaduwar cutar COVID-19 ta haddasa asara ga aikin samar da kayayyaki na kasa da kasa, da bukatun al'umma. Shugaba Xi Jinping ya sha yin kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin magance koma bayan da tattalin arzikin duniya ke fuskanta. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China