Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zhang Guimei da abokan aikinta sun inganta rayuwar 'yan mata masu yawa
2020-07-14 14:22:48        cri


Makarantar sakandare ta mata ta Huaping ta gundumar Huaping ta birnin Lijiang na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, ita ce makarantar sakandare ta mata ta farko ta gwamnati a nan kasar Sin dake koyar da dalibai kyauta. Makarantar ta karbi dalibai mata dake zaune a yankuna masu tsaunuka wadanda ba su iya ci gaba da karatunsu ba bayan kammala karatun makarantun midil da ake ba da ilmin tilas. A cikin shekaru 12 da kafa makarantar, akwai dalibai mata 1645 da suka ci jarrabawar shiga jami'o'i ko kwalejoji. A shekarar 2019, yawan daliban makarantar da suka ci jarrabawar shiga jami'o'i ya kai kashi 82.37 cikin 100 na daukacin daliban makarantar da yawansu ya kai 118. Adadin da ya sanya makarantar zama ta farko a birnin Lijiang. Maki mai kyau da makarantar ta samu sakamakon kokarin shugabar makarantar Zhang Guimei, wadda ita ce ta kafa makarantar. 

Zhang Guimei, mai shekaru 63 a duniya, wadda ta fito daga yankin dake arewa maso gabashin kasar Sin, tun tana da shekaru 17, ta tafi lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin domin amsa kiran manufar kasar Sin ta tallafawa yankunan dake kan iyaka. Daga baya, ita da mijinta suka soma aikin ba da ilmi a makarantar sakandare ta farko ta garin Xizhou dake jihar Dali mai cin gashin kansa na kabilar Bai. Mijinta dan asalin Xizhou ne, da ma Zhang Guimei tana tunanin za ta zauna ta kuma yi aiki a nan har abada. Amma, a shekarar 1996, mijinta ya rasu sakamakon ciwon sankarar tumbi. Wannan ya sa Zhang Guimei ta gabatar mahukuntan jihar Dali takadar rokon barin aiki, inda aka tura ta zuwa makarantar al'umma ta gundumar Huaping ta birnin Lijiang, don gudanar da aikin ba da ilmi.

 

Sai dai Zhang Guimei ta gano cewa, akwai bambanci a tsakanin yanayin ba da ilmi na wurin da na jihar Dali. Wasu dalibai sun ci shinkafa ko burodin da aka turara kawai, saboda ba su da kudin sayen kayan lambu, wasu dalibai mata kuma sun bar makarantar don yin aure……Da ganin haka, Zhang Guimei ta ji tausayi sosai, ta kuma tsaida kudurin cewa, za ta taimake su don su ci gaba da karatunsu.

"Na nemi taimako daga wajen jami'an kauyensu, don su tuntube su da iyalan wadancan dalibai mata na ajina, na gaya musu cewa, dole ne na komar da daliban makaranta, na kuma yi alkawarin cewa, ba su bukatar biyan kudin karatu ba, ni ce zan biya."

Amma, kudin shiga da Zhang Guimei ta samu ba su yi yawa ba, yaya za ta taimakawa wadannan dalibai mata?

"Albashi na ba shi da yawa, don haka na rage kudin da nake kashewa. Akwai dalibai sama da 50 a ajina, ba zan yarda su dakatar da karatunsu ba, saboda ba za su iya biyan kudin karatu ba, na yi iyakacin kokari na don na ga sun dawo makaranta."

A shekarar 2001, an kafa cibiyar samar da alheri ga yara ta Huaping, mai tallafawa cibiyar ya nada Zhang Guimei a matsayin shugabar cibiyar. Daga cikin yaran dake cibiyar akwai jarirai mata, wadanda iyayensu su ka bar su, hakan ya sa Zhang Guimei wadda ba ta da yaya zama mahaifiyarsu. Abubuwan da ta gano a cibiyar da makarantar sakandare ta al'umma sun sanya Zhang Guimei tunani, wato kafa wata makarantar sakandare ta mata wadda za ta rika koyar da dalibai kyauta.

 

 

Amma, cimma wannan buri ba abu ne mai sauki ba. Ga wadancan iyalai masu fama da talauci dake zaune a yankuna masu tsaunuka, ana nuna fifiko kan 'ya'ya maza, saboda rashin isassun kudi, su kan yi watsi da makomar 'ya'yansu mata. Ban da wannan kuma, gundumar Huaping ma ba ta da isassun kudaden da za ta daukin nauyin aikin ba da ilmi. Don haka, jama'a na kallon, kafa wata makarantar sakandare ta mata da za ta rika koyar dalibai kyauta, a matsayin rashin hankali

"A lokacin na yi kamar ba ni da wayo. Na yi tsammani cewa, idan wannan aikin da na gabatar yana da kyau, to zan samu goyon baya. Don haka, zan iya tattara kudin da nake bukata."

A ina ne Zhang Guimei ta tattara kudin?

"Na shiga dukkan sassan birnin don neman kudi, na zama kamar almajira. A lokacin, na samu lambar yabo ta fiffitaciyar malama, na dawo da dukkan takardun shaidar da na samu, tare da wani karamin yara dake cibiyarmu a baya na. Na kan gayawa duk wadanda na gamu da su, cewa, ina son kafa wata makaranta ce, ko za ka taimaka mana da abin da ya samu?"

Amma, amsar da ta kan samu ita ce, "kina da hanaye da kafafu, me ya sa ki ke neman zaluntar mutane?"

Daga shekarar 2002 zuwa shekarar 2007, Zhang Guimei ta yi amfani da lokacin hutu na lokacin zafi da na sanyi don tattara kudi a sauran birane, amma kudin da ta samu kadan ne, ba za su iya biyan bukatunta na kafa makaranta ba.

A shekarar 2007, Zhang Guimei ta zama wakiliyar babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 17, a yayin da ta halarci taron a Beijing, wandon da ta sanya ma ya kode, hakan ya jawo hankalin wata 'yar jarida, wadda kuma ta soma fahimtar labarin Zhang Guimei. Daga baya, wani rahoto mai taken "Ina da wani buri" ya sanya labarinta da burinta na kafa wata makarantar sakandare ta mata ta karade kasar baki daya. Goyon baya da daukacin kasar ta nuna mata ya taimakawa Zhang Guimei wajen cimma burinta. A watan Agusta na shekarar 2008, an kammala aikin kafa makarantar sakandare ta mata ta Huaping. Zhang Guimei ta zama shugabar makarantar.

A shekarar farko, makarantar ta dauki dalibai mata 100, yawancinsu 'yan kananan kabilu ne. Saboda dukkansu sun shiga makarantar ba tare da jarrabawa ba, yawancinsu ba su da tushen karatu sosai, Zai wuya su samu makin da ake bukata.

 

"A yayin da na ziyarci gidajen dalibai na, iyayensu ko kakanninsu su kan gaya min cewa, 'ya'yansu sun shiga makarantar sakandare, hakan ya kwantar musu da hankali. Lallai, ilmi na da muhimmanci a zuciyarsu."

Zhang Guimei ta kara niyyarta ta kara makin karatu na dalibansu. Bisa shirin da ta tsara, daliban za su tashi da karfe 5 da safe, su kuma yi barci bayan karfe 12 da dare, cikin mintoci uku ne kawai dalibai za su isa dakin cin abinci daga aji, kuma ana bukatar su kammala cin abinci a cikin mintoci 10.

Lallai dalibai sun sha wahala sosai, amma Zhang Guimei da malaman makarantar fa?

"Kokarin ya bambanta da na sauran malamai dake wasu makarantu. Wani malamin ya yi aure, amma bayan kammala bikin aure, ya koma makaranta ba tare da bata lokaci ba. An yiwa wata malama tiyata kafin ta haihu, sai na gaya mata cewa, ki huta sosai, amma ta gaya min cewa, idan likita ya ce, zan iya sanya tufaffi, to zan komo, ba na bukatar na daina aiki."

 

Bisa kokarin da dukkan malamai da dalibai suka yi, yawan daliban da suka ci jarrabawar shiga jami'a ya zama na fako a birnin.

Kamar yadda Zhang Guimei ta fada,

"Abun da muka bayar shi ne rayuwanmu. Ganin yaddai dalibanmu suke kokarin inganta rayuwar al'umma bayan da suka kammala karatunsu a jami'a, ya sa na gamsu. Idan makomarsu ta fi tawa kyau, kuma sun fi ni jin dadin zaman rayuwa, buri na ya cika ."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China