Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An cika shekara guda da kaddamar da yankin ciniki maras shinge na Afirka
2020-07-14 13:59:02        cri

A ranar 7 ga watan Yulin shekarar 2019, an gudanar da taron kolin kungiyar tarayyar Afirka karo na 12 a birnin Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijer, inda aka sanar da fara kafa yankin ciniki maras shinge na Afirka. Yanzu shekara guda ke nan, kuma ban da Eritrea, dukkanin kasashe mambobin kungiyar sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta nahiyar Afirka, kuma daga cikinsu, hukumomin kafa dokoki na wasu kasashe 30 sun zartas da yarjejeniyar. Aikin kafa yankin ciniki maras shinge na Afirka ya shaida niyyar kasashen Afirka ta samar da kasuwar bai daya da kuma aiwatar da hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban. Bisa ga yarjejeniyar, kasashen da suka daddale yarjejeniyar za su daina sanyawa juna kudin kwastan da ya kai kaso 90% nan da shekaru 5 zuwa 10 masu zuwa, baya ga kawar da shingayen ciniki da suka kafa ta sauran fannoni.

Sai dai a yayin da annobar Covid-19 ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, su ma kasashen Afirka ba su tsira ba. Alkaluman da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Afirka ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa ranar 11 ga wata, akwai mutane 543136 da aka tabbatar sun kamu da cutar, a yayin da wasu 12474 sun mutu a sakamakon cutar.

A halin yanzu, kasashen Afirka kalilan ne suka "bude kofarsu" a dukkanin fannoni, misali kasar Tanzania, a yayin da akasarin kasashen ke ci gaba da daukar matakai na takaita zirga-zirgar mutane.

A sakamakon cutar, saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya ya ragu, wanda kuma ya haifar da babban tasiri ga kasashen Afirka. A kwanan baya, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya rage hasashen da ya yi kan bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka da ke kudu da Sahara. A rahoton da asusun ya fitar, alkaluman GDP na yankin zai ragu da kaso 3.2% a wannan shekara, a yayin da bankin duniya a rahoton da ya fitar ya yi hasashen raguwar kaso 2.8% na GDP a yankin. Kasancewarsu manyan ginshikai biyu na tattalin arzikin Afirka, asusun IMF da bankin duniya dukkansu sun yi hasashen koma bayan tattalin arziki da Nijeriya da Afirka ta kudu za su fuskanta.

A hakika, annobar Covid-19 na haifar da kalubale ga Afirka da ma duniya baki daya. A cikin irin wannan yanayi kuma, aikin kafa yankin ciniki maras shinge a Afirka na da muhimmiyar ma'ana ta fannin bunkasa tattalin arzikin nahiyar da ma tinkarar matsalar annobar.

Cinikin da kasashen shiyyar ke yi tsakaninsu ya kasance wani muhimmin bangare na bunkasuwar tattalin arzikin shiyyar, wanda kuma ya ke kare tattalin arzikin shiyyar daga shiga matsalar tattalin arziki da ake fuskanta daga ketare.

Sai dai rahoton da taron MDD kan ciniki da ci gaba(UNCTAD) ya fitar, ya nuna cewa, a shekarar 2017, yawan kayayyakin da kasashen Afirka suka fitar ga juna ya kai kaso 16.6% na gaba dayan kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasashen ketare, a yayin da adadin ya kai kaso 68.1% a nahiyar Turai da kuma kaso 59.4% a Asiya, sai kuma kaso 55.0% a nahiyar Amurka.

Rashin ingancin ayyukan jigilar kayayyaki da koma bayan kayayyakin more rayuwa da shingayen ciniki da aka kafa a fannin kudin kwastan su ne suke yi wa cinikin da ke tsakanin kasashen Afirka tarnaki, musamman ma abubuwan more rayuwa. A halin da ake ciki yanzu, babu isassun layukan dogo a kasashen Afirka, ana kuma fuskantar komar bayan hanyoyin motoci, lamarin da ya haifar da rashin ingancin aikin jigilar kayayyaki. Ban da wannan, matsalar karancin samar da wutar lantarki ma tana hana ci gaban tattalin arzikin nahiyar.

Amma a wannan fanni na abubuwan more rayuwa, kasar Sin tana da kwarewa, haka kuma tana da kudin jari da na'ura da kuma fasahohi masu inganci. A hakika, Sin da kasashen Afirka sun cimma nasarar gudanar da jerin shirye-shirye na ayyukan more rayuwa, ciki har da hanyoyin dogo da na mota da gadoji da kuma tashoshin ruwa, wadanda a sa'i daya suka taimaka ga inganta abubuwan more rayuwa a Afirka, a sa'i daya kuma, suka inganta yanayin zuba jari a kasashen.

Kasar Sin ta dade da zama abokiyar ciniki ta farko ga kasashen Afirka da ma muhimmiyar kasar da ke zuba jari a kasashen, don haka, take taka muhimmiyar rawa ta fannin sa kaimin kafa yankin ciniki mai 'yanci a Afirka da kuma dunkulewar nahiyar.

A yayin taron koli na musamman kan yaki da cutar Covid-19 da ya gudana tsakanin Sin da Afirka a watan Yunin da ya gabata, kasar Sin ta bayyana cewa, idan har aka son tinkarar annobar, ya kamata Sin da kasashen Afirka su karfafa hadin gwiwarsu bisa shawarar ziri daya da hanya daya, sa'an nan su tabbatar da sakamakon da aka cimma a yayin taron kolin na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.

Masharhanta na ganin cewa, duk da tarin kalubalen da ake fuskanta, ana sa ran za a kafa yankin ciniki maras shinge da zai hade al'ummar da suka kai biliyan 1.2 waje guda. Dunkulewar nahiyar Afirka za ta kuma sa kaimin ci gaban nahiyar, wadda kuma za ta taimaka ga gina kyakyyawar makomar al'umma ta bai daya a tsakanin sassan biyu.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China