Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya dace Sin da kasashen Larabawa su kara hada kai domin inganta tabbaci ga duniya
2020-07-13 19:39:45        cri

A kwanakin baya bayan nan, manyan jami'ai da masanan da abin ya shafa na kasar Sin, da wasu kasashen Larabawa, sun shirya wani dandalin tattaunawa mai taken "Hada kai tsakanin kasar Sin da kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya: Kara zurfafa zumuncin gargajiya tare da kiran makoma mai haske" ta kafar bidiyo, inda suka yi shawarwari kan fasahohin da sassan biyu suka samu a bangaren yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, haka kuma sun tsara shirinsu na hadin gwiwa dake tsakaninsu bayan ganin bayan annobar.

Yayin dandalin, gaba daya suna ganin cewa, huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa tana kara kyautatuwa, yayin da suke fuskantar annobar tare, don haka makomar hadin gwiwarsu tana da haske.

Hakika yayin da ake kokarin dakile annobar COVID-19, kasar Sin da kasashen Larabawa suna taimakawa juna, kuma suna gudanar da hadin gwiwa daga duk fannoni.

Kana shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba tattaunawa da takwaransa na kasar Saudiya Salman Bin Abdulaziz Al Saud, da na Qatar Tamim Bin Hamad Al-Thani, da na hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohamed Bin Zayed Al Nahyan, da na Masar Abdel Fattah Al Sisi ta wayar tarho har sau biyar, inda suka yi shawarwari kan batutuwan dake shafar kandagarkin annobar da kuma gudanar da hadin gwiwa.

Abun farin ciki shi ne, yayin da kasar Sin take shan wahalar yaduwar annobar, nan take kasashen Larabawa sun samar mata taimakon kayayyakin kiwon lafiya, kuma yayin da kasashen Larabawa suke kokarin dakile annobar, kasar Sin ita ma ta samar musu tallafi gwargwadon karfinta.

Yayin dandalin, manzon musamman na gwamnatin kasar Sin kan batun yankin Gabas ta Tsakiya Zhai Jun ya bayyana cewa, kawo yanzu gaba daya kasar Sin ta riga ta samar da maganin tantance kwayar cutar COVID-19 ga mutane miliyan 1 a yankin, kana ta samar da kayan rufe baki da hanci sama da miliyan 13 gare su.

A sa'i daya kuma, ta kira taron masana tsakaninta da kasashen Larabawa 22, tare kuma da aika tawagoyin likitoci ga kasashe takwas dake yankin.

Duk da cewa wasu 'yan siyasa na kasashen yamma suna siyasantar da annobar, har ma suna kawo illa ga hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a bangaren yaki da annobar, amma har kullum, kasar Sin da kasashen Larabawa, suna nacewa kan manufar adalci, domin kyautata tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa. A sa'i daya kuma, kasashen Larabawa suna goyon bayan matsayin kasar Sin, kan batutuwan dake shafar yankin musamman na Hong Kong, da jihar Xinjiang, da jihar Taiwan. Kaza lika kasar Sin tana goyon bayan kokarin kasashen Larabawa, na kiyaye 'yancin kai da kwanciyar hankali a kasashensu. Duk wadannan sun nuna cewa, sassan biyu wato kasar Sin da kasashen Larabawa, suna kare adalci da gaskiya a fadin duniya tare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China