Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Tibet ta taimakawa manoma da makiyaya 461,000 samun aiki
2020-07-13 15:50:51        cri

Kawo yanzu, hukumomin jihar Tibet mai cin gashin kanta dake kudu maso yammacin kasar Sin, sun taimakawa manoma da makiyaya 461,000 samun aikin yi a bana.

Hukumar kula da ma'aikata da walwalar al'umma ta yankin, ta ce kawo yanzu, ayyukan sun samar musu da kudin shigar da ya kai yuan biliyan 3.75, (kwatankwacin dala miliyan 536).

Makiyaya da manoma su suka mamaye kaso mai yawa na ma'aikatan jihar Tibet, kuma inganta basirarsu na taka muhimmiyar rawa wajen kara yawan aiki a bangaren ayyukan gona da kiwo. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China