Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda Sin ta shiga yarjejeniyar ATT zai taimaka wajen kiyaye tsaron duniya
2020-07-12 15:54:29        cri

A kwanakin baya bayan nan, Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya gabatar da takardun bukatar shiga yarjejeniyar cinikin makamai ta ATT na kasar Sin ga babban sakataren MDD Antonio Guterres.

Hakika har kullum gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci matuka kan matsalolin da fasa kaurin makamai da saba yarjejeniyar cinikin makamai ke haifarwa, kuma tana goyon bayan manufofin yarjejeniyar, kana ta amince da daukar dukkan matakan da suka dace wajen kiyaye dokokin kasa da kasa dake shafar cinikin makamai da batun kawar da fasa kaurin makamai.

Bugu da kari, a ko da yaushe kasar Sin tana daukar tsauraran matakai yayin fitar da kayayyakin aikin soji zuwa ketare, bisa ma'aunin yarjejeniyar cinikin makamai ta ATT, wadda ta fara aiki a hukumance a ranar 24 ga watan Disamban shekarar 2014.

A bayyane an lura cewa, makasudin shiga yarjejeniyar ATT na kasar Sin shi ne domin daidaita batutuwan dake shafar cinikin makamai tsakanin kasa da kasa, da kiyaye tsaro da zaman lafiya a fadin duniya tare da sauran kasashe, ta yadda za a cimma burin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama.

A halin yanzu, manyan batutuwan da suka fi jawo hankulan al'ummun kasa da kasa su ne tabbatar da zaman lafiya da kuma samun ci gaba, to idan ana son tabbatar da tsaron duniya, ya zama dole a daidaita batun cinikin makamai tsakanin kasa da kasa bisa yarjejeniyar da kasashen duniya suka kullu, don haka a ranar 7 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara karfafa cudanya da hadin gwiwa dake tsakaninta da sauran kasahe domin aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, tare kuma da kyautata tsarin cinikin makamai tsakanin kasa da kasa, sa'an nan tana son taka karin rawa wajen kiyaye zaman lafiya da samun ci gaba a fadin duniya.

Haka zalika, babban wakilin kula da harkokin diplomasiyya da manufofin tsaro na kungiyar tarayyar kasashen Turai Josep Borrell Fontelles shi ma ya yi tsokaci cewa, shigar kasar Sin cikin yarjejeniyar cinikin makamai zai taimaka wajen tabbatar da adalci yayin da ake gudanar da cinikin makamai tsakanin kasa da kasa, haka kuma zai taimaka wajen kiyaye tsaron duniya baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China