Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tabbas janyewar Amurka daga WHO za ta kawo illa ga sha'anin kiwon lafiya na Afirka
2020-07-10 18:44:47        cri

A ran 7 ga watan Yuli ne, kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya shelanta cewa, a ran 6 ga wata, bangaren Amurka ya sanar wa babban sakataren MDD kudurin kasar Amurka na janyewa daga WHO a hukumance, wannan kuduri zai fara aiki a ran 6 ga watan Yulin shekarar 2021. Gwamnatin kasar Amurka ta tsai da kudurin janyewa daga WHO ne a lokacin da kasar Amurka ita kanta da sauran sassan duniya suke cikin mawuyacin hali wajen dakile yaduwar annobar COVID-19. Wannan kuduri ya sake bayyana yadda manufar "mayar da USA a gaban kome" da kasar Amurka ke dauka take kare moriyar kasar Amurka kawai.

A ran 21 ga watan Yunin shekarar 1948, kasar Amurka tana daya daga cikin kasashe wadanda suka kulla yarjejeniyar kafa hukumar kiwon lafiya ta kasa ta kasa, wato WHO. Sakamakon haka, ya zuwa yanzu, kasar Amurka ta kasance wadda ta fi ba da tallafin kudi karo-karo mafi yawa ga hukumar, inda aka tabbatar da cewa, kasar Amurka ta bayar da gudummawa matuka ga kungiyar WHO, da ma sha'anin kiwon lafiya na duniya. Amma yanzu an gane cewa, a hakika, kasar Amurka tana baiwa kungiyoyin kasa da kasa tallafin kudi ne saboda manufofinta na diflomasiyya, amma ba domin jin kai ba. Kuma an gane cewa, idan kasar Amurka ta janye daga WHO, tabbas hakan zai kawo illa sosai ga galibin kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka wajen dakile wasu cututukan da suke addabar nahiyar, ciki har da annobar COVID-19.

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, kawo ran 9 ga watan Yulin, yawan wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasashen Afirka ya wuce dubu 500, a yayin da mutane kusan dubu 12 suka mutu sakamakon cutar. Hukumar WHO ta taba yin hasashen cewa, idan har aka kasa shawo kan annobar, a ciki farkon shekara, yawan mutanen da suka mutu ko za su mutu sakamakon cutar zai kai kusan dubu 200, yawan mutanen da za su harbu da cutar zai kai miliyan 44. Sakamakon haka, yanzu kasashen Afirka na cikin mawuyacin hali mai tsanani wajen dakile cutar, suna bukatar taimako daga hukumar WHO da sauran kasashen duniya cikin gaggawa.

Ba ma kawai kasar Amurka, wato kasa mafi karfin ci gaban tsarin kiwon lafiya a duk duniya, tana samar da tallafi mafi yawa ga hukumar WHO ba, tana kuma da ma'aikatan kiwon lafiya mafi yawa a cikin hukumar, wasu hukumomin nazarin cututtuka na kasar Amurka suna kuma taimakawa hukumar WHO wajen dakile cututuka iri iri. Idan kasar Amurka ta janye daga hukumar a hukumance gaba daya, tabbas wadannan ma'aikata da hukumomin kiwon lafiyarta su ma za su fice daga hukumar. Lamarin zai kawo illa kwarai ga aikin WHO, da ma sha'anin kiwon lafiya na kasashe wadanda ba su da karfin tattalin arziki, musamman kasashen Afirka wadanda ba su da ingantattun tsarin kiwon lafiya na yau da kullum.

Kamar yadda Hausawa kan ce, "hannu daya ba ya daukar daki". A lokacin da muke kokarin dakile annobar COVID-19, akwai bukatar dukkan kasashen duniya, ciki har da kasar Amurka su kara yin hadin gwiwa domin ta yadda za mu cimma burinmu na a gudu tare a tsira tare a a yayin da ake fuskantar kalubalen annobar. Duniya na fatan kasar Amurka za ta mai da hankalinta kan abubuwan da sauran kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa suke kulawa, za ta iya sauke nauyi na kasa da kasa da ke bisa wuyanta kamar yadda ya kamata. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China