Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fasahar Juncao dake taimakawa kau da talauci a duniya
2020-08-14 15:16:39        cri

 

 

Wani labari a shafin Internet ya bayyana cewa, kasar Afirka ta tsakiya ta gudanar da bikin cika shekaru 61 na kafuwar kasar, a watan Disamban bara, inda shugaban kasar Faustin Touadéra ya mika lambobin yabo ga wasu Sinawa 6, wadanda suka yada fasahar Juncao a kasar. A cewar shugaban, wannan fasaha za ta taimakawa kasar Afirka ta Tsakiya raya aikin gona, da rage talauci, da kyautata muhallin kasa, don haka a madadin jama'ar kasarsa ya yi wa wadannan kwararru na kasar Sin godiya.

To, ganin wannan labari ya sa ni sha'awar fasahar Juncao. Mene ne fasahar Juncao? Kuma me ya sa gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya ke dora muhimmanci matuka kan fasahar, har ma ta baiwa wasu kwararru Sinawa masu kula da fasahar manyan kyaututtuka?

Hakika idan mun dubi kalmar "Juncao", za mu iya raba shi zuwa "Jun", wato "laimar kwadi" a bakin Sinawa, gami da "Cao", wato ciyayi. Ta wannan hanya, za mu iya fahimtar ma'anar kalmar Juncao, wadda ita ce "Ciyayin da ake yin amfani da su wajen samar da laimar kwadi".

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China