Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dokar tsaron kasa mai nasaba da Hong Kong na ci gaba da samun yabo
2020-07-09 15:29:02        cri

Kamar yadda dukkanin masu bibiyar manyan kafofin watsa labaru na kasa da kasa suka ji, a jiya Laraba ne aka kaddamar da ofishin da zai lura da aiwatar da dokar tsaron kasar Sin mai nasaba da yankin Hong Kong. Dokar da ta samu amincewa daga majalissar wakilan jam'ar kasar Sin, aka kuma kaddamar da ita ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata.

Babban nauyin da ke wuyan wannan sabon ofis dai shi ne nazarta, da kuma sanya ido kan ci gaban da ake samu, game da aiwatar da wannan doka a yankin na Hong Kong. Kaza lika ofishin zai rika gabatar da mahangarsa, tare da bayyana matsaya kan muhimman manufofi, da sanya ido, da ba da jagoranci, da taimakawa yankin Hong Kong, wajen tabbatar da nasarar aiwatar da wannan muhimmiyar doka ta tsaron kasa.

Sanin kowa ne dai cewa, an samar da wannan doka ne bayan shafe tsawon lokaci yankin na Hong Kong na fuskantar kalubale daga masu tada kayar baya, da 'yan a ware, wadanda wasun suke samu taimako daga kasashen ketare, da nufin haifar da baraka, da gurgunta ci gaban kasar Sin.

Kamar dai yadda Bahause kan ce "Biri ya yi kama da mutum", domin kuwa tun ma kafin wannan doka ta kai ga matakin kaddamarwa, wasu kasashen yamma, da 'yan siyasarsu, suka fara nuna adawa da ita, suna fakewa da hakkin bil Adama domin sukar gwamnatin kasar game da wannan doka. Alhali ba wata kasa mai 'yanci a duniya, da za ta kauda kai ta bari wani yanki nata ya fada yanayin tarzoma, da tashin hankali da zaman ta ci barkatai, ba tare da ta dauki wani mataki na shawo kan hakan ba.

Amma idan mun yi duba na tsanaki, za mu ga cewa, da yawa daga irin wadannan kasashe masu son shafawa kasar Sin kashin kaji, suna da makamanciyar wannan doka da suke amfani da ita, wajen tabbatar da tsaro da wanzar da zaman lafiya.

Fahimtar hakan ne ma ya sa, dokar tsaron kasa da kasar ta Sin ta kaddamar ke ci gaba da samun karbuwa, da yabo daga sassa da dama. Da yawa daga masharhanta sun bayyana ta, da doka wadda ta zo a gabar da yankin Hong Kong ke matukar bukatar ta.

A cikin gida, wannan doka ta samu karbuwa daga al'ummun Hong Kong, inda alkaluman wani binciken jin ra'ayin jama'a na baya bayan nan ya nuna cewa, kaso 66 bisa dari na al'ummar Hong Kong na goyon bayan wannan doka.

Daga sauran sassan kasashen duniya ma, kama daga nahiyar Afirka, da wasu sassan na kasashen Larabawa, har ma zuwa wasu bangarori na masana dake kasashe masu sukar dokar, akwai kyakkyawar fahimta game da muhimmancin dokar.

Masharhanta da dama sun bayyana wannan doka, a matsayin ginshikin aiwatar da tsarin nan na "kasa daya mai bin tsarin mulki biyu" a Hong Kong. Kudurin da ba zai taba samun nasara ba, muddin yankin ya ci gaba da kasancewa a yanayi na ta ci barkatai.

Wasu masana da suka yabawa dokar, na ganin baya ga ita kanta kasar Sin, sauran sassan kasa da kasa ma za su ci gajiyar managarcin yanayin da Hong Kong zai shiga ba da jimawa ba, sakamakon aiwatar da wannan doka, ta yadda masu zuba jari, da sauran fannonin tattalin arziki za su cimma moriyar zaman karbo a yankin.

Ko ba komai ma dai, yankin Hong Kong bangare ne na kasar Sin, wanda ba zai taba yiwuwa a balle shi ba. Don haka dukkanin wasu dokoki, da ka'idojin da za a aiwatar a yankin, na da nasaba ne ta kai tsaye, da harkokin cikin gidan kasar Sin. Kuma bai dace wata kasa ta daban, ta rika tsoma baki cikin wannan harka ba. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China