Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ilimi hasken Rayuwa
2020-07-08 16:17:46        cri

A ranar Talata 7 ga watan Yulin wannan shekara ce, kimanin dalibai miliyan goma suka rubuta jarrabawar shiga kwalejoji na wannan shekara a kasar Sin da ake kira 'GAOKAO'. Koda yake jarabawar ta wannan shekara ta bambanta da na shekarun baya, saboda annobar COVID-19. Ganin cewa, wannan shi ne taron jama'a mafi yawa da aka shirya a kasar, tun barkewar annobar COVID-19. Ya sa kasar Sin ta dauki dukkan matakan da suka dace na ganin an gudanar da wannan muhimmiyar jarrabawa cikin nasara da ma kiyaye lafiyar dalibai.

Wasu daga cikin wadannan matakai da mahukuntan na kasar Sin suka dauka, don ganin komai ya gudana lami lafiya.

Bugu da kari, sassa daban-daban na kasar Sin sun dauki mabanbanta matakan kare lafiyar dalibai. Kamar a Beijing da Tianjian, da Jinan, lardin Shandong da lardin Shanxi, duk sun tanadi wuraren gwaji da killace wadanda ka iya nuna alamomi na rashin lafiya ko zazzabi har ma an tanadi kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya, don magance duk wani abin da ka je ka zo.

Muhimmin sako a jarabawar ta bana, shi ne, "Zaman lafiya" da kuma "Adalci". Kasancewar jarabawar zama wani mafarin canja rayuwa a dukkan fannoni. Wannan ne ma ya sa a farkon shekarar 2003, Xi Jinping, a lokacin da ya rike da mukamin sakataren jam'iyya na lardin Zhejiang, ya taba cewa, "Abin alfahari ne, dalibi ya samu damar shiga jami'a, amma ba lallai ba ne a nuna damuwa ko zakuwa idan ba a yi nasarar shiga ba. Nasara tana hannunka. Hanyar samun kaiwa ga nasara, ba sai mutum ya shiga kwaleji ko bai shiga ba, abu mafi muhimmanci, shi ne abin da zai iya yi a zahiri" wato kowa da irin basirar da Allah ya ba shi.

Saboda muhimmancin wannan jarabawa, ya sa ma'aikatar Ilimi ta kasar Sin, ta tanadi wasu lambobi, inda za a tuntubi sassan kula da harkokin mulki da daukar dalibai da hukumomin shirya jarabawa a larduna 31, yankuna masu cin gashin kansu da birane dake karkashin gwamnatin tsakiya kai tsaye, don tabbatar da adalci da daidaito a jarabawar. Idan kana Kyau aka ce ka kara da Wanka.

Hakika, ci gaban kasar Sin a halin yanzu, ya haifar da hanyoyi da dama na samun nasara a rayuwa. Ba lallai ne sai kowa ya shiga makaranta ba, yanzu haka bunkasuwar harkar Intanet a kasar Sin, ta taimakawa masu kananan sana'o'i da karamin kafi nesa ba kusa ba. Yanzu muna wani zamani ne da fasahar sadarwa ta karade dukkan fannoni na rayuwa, kowa yana iya shiga duniyar gizo, ya kuma ci gajiyar bangaren ta hanyar da ta dace da shi. Don haka, duk wani bangare na rayuwa, muddin suna samun kudin shiga, ko ma'aikacin gwamnati, ko masu aiki mai gwabi, har da manoma, sauran 'yan kasa, duk za su iya rufa asirinsu har ma a mutunta su, kuma suna da 'yancin yin rayuwa cikin farin ciki. A takaice dai, idan mutum yana da sana'ar da zai dogara da ita, yana kuma samun abin da zai kai bakin salati, bukata ta biya, kuma ba sai an shiga makaranta ba, domin masu neman shiga makarantar suna da yawa. Kuma guraben da aka tabadar kalilan ne.

Daga karshe, shugaba Xi ya yiwa dalibai miliyan 10.71 da suka rubuta jarawabar shiga kwalejoji ta kasa ta wannan shekara fatan alheri. Yana kuma fatan ji daga gare su a koda yaushe. Yara manyan gobe. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China