Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa cikin sauri
2020-07-08 13:24:34        cri

 

Babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a jiya Talata cewa, har yanzu cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa cikin sauri, kana wannan saurin yaduwar bai kai wani matsayi na koli ba tukuna.

Mista Tedros Ghebreyesus ya yi gargadi kan saurin yaduwar cutar COVID-19 a duniya, a yayin wani taron manema labaru, inda ya ce,

"A lokacin da aka fara samun barkewar cutar, an kwashe makwanni 12, kafin a samu masu kamuwa da cutar da suka kai dubu 400.

Amma a karshen makon da ya wuce, an riga an samu karin wasu fiye da dubu 400 da suka harbu da cutar. Zuwa yanzu, wasu mutane miliyan 11.4 sun taba kamuwa da cutar, kana daga cikinsu, fiye da dubu 535 sun rasa rayukan su. Har yanzu cutar na kara yaduwa cikin sauri, ba mu kai wani matsayin koli na saurin yaduwarta ba tukuna."

Mike Ryan, shi ne darektan zartaswa mai kula da ayyukan gaggawa masu nasaba da lafiyar jama'a, a hukumar WHO, wanda shi ma ya bayyana cewa, tsakanin watan Afrilu da watan Mayun da ya gabata, a kan samu karin wasu mutum dubu 100 a kowace rana, amma zuwa yanzu, wannan adadi ya kai kimanin dubu 200. Ya yi gargadin cewa, sakamakon karuwar sabbin masu kamuwa da cutar, yawan mutanen da suka mutu shi ma zai karu. Ya ce,

"A watan Yulin da muke ciki, ana ganin yadda sabbin masu kamuwa da cutar ke karuwa cikin sauri, amma yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar bai karu sosai ba. Dalilin da ya sa haka shi ne, bayan da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar, ba za a samu karin mutanen da suka mutu nan take ba. Ana bukatar lokaci kafin a iya ganin wani mummunan tasiri. Ba mu fara samun karuwar wadanda suka kamu da cutar cikin sauri ba, har zuwa cikin makwanni 5 zuwa 6 da suka wuce. Saboda haka, idan mun samu karin mutanen da suka rasu sakamakon cutar nan ba da dadewa ba, ba zan yi mamaki ba."

Ban da wannan kuma, a yayin taron na manema labaru, jami'an hukumar WHO sun amsa tambayar da aka yi, game da yiwuwar yaduwar kwayoyin cutar COVID-19 cikin iska. Kafin hakan, wasu masanan ilimin halittu 239 daga kasashe 32, sun rubuta wata wasika ga hukumar WHO, inda suka bukaci hukumar da ta kara mai da hankali kan hadarin da ake fuskanta, dangane da samun yaduwar cutar COVID-19 ta iska.

A cewar wadannan masana, hukumar WHO ba ta taba dora muhimmanci, gami da watsa wani cikakken bayani, kan yiwuwar kasancewar kwayoyin cutar COVID-19 cikin iska, da yiwuwar yaduwar cutar ta hanyar iska ba. Sai dai karin shaidun da aka samu sun nuna cewa, yaduwa ta iska ka iya zama wata muhimmiyar hanyar da kwayoyin cutar COVID-19 suke bi wajen bazuwa.

A nata bangare, jami'ar hukumar WHO mai kula da aikin rigakafin cuta da shawo kan yaduwarta, Benedetta Allegranzi, ta tabbatar da cewa ana samun karin shaidu game da yaduwar cutar COVID-19 ta iska. Sa'an nan ta ce,

" Ana kara kokarin bincike a wannan fanni, tare da samun karin shaidu, amma har yanzu ba su iya tabbatar da gaskiyar ikirarin ba. Don haka, a wannan halin da muke ciki, ba za mu iya kawar da yiwuwar samun yaduwar cutar COVID-19 ta hanyar iska a wasu wuraren da ake da cunkoson jama'a ba. Musamman ma karkashin wasu yanayi na musamman, misalin samun cunkuson mutane, da kasancewa cikin wani rufaffen muhalli, inda ba a samun gudanar iska sosai. Duk da haka, ana bukatar kara tara bayanai da shaidu, da nazari a kansu. Sa'an nan hukumar WHO a nata bangare, za ta ba da taimako kan aikin."

An ce, hukumar WHO tana musayar raya'yi tare da masanan kasashe daban daban, kan batun samun yaduwar cutar COVID-19 ta hanyar iska, sa'an nan tana shirin gabatar da wani rahoto cikin kwanakin nan, don bayyana cikakkun hanyoyin da cutar ke bi, don samun yaduwarta tsakanin mutane. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China