Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Inganta Hadin-Gwiwar Sin Da Indiya Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Kan Iyakokinsu Ya Dace Da Muradunsu
2020-07-07 20:11:11        cri

Kwanan nan, wakili na musamman na kasar Sin kan batun iyakokin kasashen Sin da Indiya, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya zanta da wakilin musamman na Indiya, kana mashawarcin kasar ta fannin tsaron kasa, Ajit Doval ta wayar tarho, inda suka cimma matsaya tare domin sassauta halin ja-in-ja tsakaninsu dangane da batun iyakokin kasa, al'amarin da ya shaida niyyar bangarorin biyu ta daidaita sabani ta hanyar yin shawarwari, matakin da ya karfafa gwiwar ci gaba da raya dangantaka tsakanin Sin da Indiya da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya baki daya.

Rikicin da ya barke a kan iyakokin Sin da Indiya a watan Afrilu, ya jawo hankalin kasa da kasa. A matsayinsu na makwabtan juna, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kan iyakokin kasashen biyu, ya dace da muradunsu dukka, kuma samun ci gaban kasa shi ne babban aiki mafi muhimmanci ga kasashen biyu. Alal misali, kasar Sin tana shirin kawar da kangin talauci baki daya a karshen shekarar da muke ciki, da cimma burin raya al'ummar kasar mai matsakaicin wadata, tare kuma da habaka bude kofarta ga kasashen waje daga dukkan fannoni. Ita ma kasar Indiya, tana shirin raya tattalin arzikinta da darajarsa zata kai dala triliyan 5 zuwa nan da shekarar 2025, abun da ya sa kasar zama daya daga cikin kasashe mafi karfin tattalin arziki a duniya. Ganin yadda kasashen biyu ke da kamanceceniya da dama a fannin neman bunkasuwa, ya zama dole su dakatar da yiwa juna barazana, a maimakon haka, su karfafa hadin-gwiwa.

Musamman a daidai wannan lokaci da cutar COVID-19 ke dada bazuwa a fadin duniya, akwai kasashe da dama ciki har da Indiya, wadanda suke fuskantar babban matsin lamba a fannonin da suka jibanci dakile yaduwar cutar da farfado da tattalin arziki, don haka, duk wani yunkuri na lalata dangantakar Sin da Indiya zai iya tsananta halin da ake ciki.

A dayan bangaren kuma, Sin da Indiya muhimman kasashe ne wadanda suka taimaka sosai ga habakar tattalin arzikin duniya, wato idan sun iya daidaita sabanin dake tsakaninsu da kara gudanar da shawarwari, hakan zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China