2020-07-06 20:44:12 cri |
Kalaman Francisca sun shaida cewa, rigakafi ya fi magani a yayin da ake yakar ta'addanci. Idan ana son kawar da tushen ayyukan ta'addanci, akwai bukatar raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma. Amma a tunanin sakataren harkokin wajen Amurka wato Mike Pompeo, ba haka lamarin yake ba, saboda kwanan nan, ya sake zargin kasar Sin cewa, wai ana tursasawa gami da kame dimbin fursunoni a jihar Xinjiang, a wani yunkuri na shafawa gwamnatin kasar kashin kaji kan kwararan matakan da ta dauka na yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi.
Hakikanin gaskiya, kalaman Pompeo ba su da tushe balle makama. Kamar yadda kasashen duniya da dama ke ganin cewa, batutuwan da suka jibanci jihar Xinjiang, ba batutuwa ne da suka shafi hakkin dan Adam ko wata kabila ko kuma wani addini ba, amma batutuwa ne da suka shafi yaki da ayyukan ta'addanci da masu yunkurin kawowa kasar Sin baraka. Domin daidaita wadannan matsaloli tun daga tushensu, gwamnatin kasar tana iyakacin kokarinta wajen inganta samar da ilimi da isassun ayyukan yi. Kuma shaidu sun nuna cewa, taimakawa 'yan kananan kabilu samun guraban ayyukan yi na daya daga cikin muhimman matakan da aka dauka domin tabbatar da hadin-kai da zaman lafiya gami da bunkasuwa a jihar ta Xinjiang.
A kwanan nan, akwai kasashe da dama wadanda suka sake jaddada goyon-bayansu ga manufofin gwamnatin kasar Sin kan jihar Xinjiang. Kuma 'yan kasashen waje da dama da suka taba kai ziyara jihar, sun nuna cewa, ayyukan yakar ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi da kasar Sin take gudanarwa, abubuwan koyi ne ga kasashen duniya.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China