Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta taimakawa Benin da kayayyakin yaki da COVID-19
2020-07-04 15:36:27        cri

Ofishin jakadancin kasar Sin a Jamhuriyar Benin, ya bada gudunmawar adadi mai yawa na kayayyakin tsafta ga majalisar dokokin kasar, a matsayin wani bangare na aikin yaki da COVID-19 a kasar.

Jakadan kasar Sin a Benin, Peng Jingtao, ya ce gudunmawar wata hanya ce ta kasar Sin, ta nuna goyon baya ga al'ummar Benin da ma majalisar, a yakin da suke da annobar.

Da take karban kayayyakin, mataimakiyar shugaban majalisar, Mariama Zime Tallata, ta bayyana godiya ga ofishin jakadancin da ma al'ummar Sinawa, a madadin 'yan majalisar. Tana mai cewa, suna yabawa da kulawar da Sin ke ba al'ummar kasar a ko da yaushe, musamman yayin yaki da annobar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China