Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalilin da ya sa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kara kuzari ba tare da tsayawa ba
2020-07-01 19:26:27        cri

Ran 1 ga watan Yuli na wannan shekara, rana ce ta cika shekaru 99 da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. A cikin wadannan shekaru 99, 71 daga cikinsu, kasar Sin na karkashin jagorancin JKS, a kuma wannan tsakani jam'iyyar ta samu karin mambobi har miliyan 91, wadannan alkaluma sun bayyana tarihi mai armashi, na wannan jam'iyya mafi girma a duniya, da kuma dalilin da ya sa jam'iyyar ta kara kuzari a cikin dogon lokaci ba tare da tsayawa ba.

To ko mene ne dalilin da ya sa JKS ta iya cimma wadannan nasarori? Duk duniya na kokarin neman dalili.

Kamar yadda shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ya sha jaddada, cewar tun ranar kafuwar JKS, ba ta son kai ko kadan, aikin ta shi ne ta yi namijin kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a.

A halin yanzu da muke tsaka da yakar COVID-19, an bayyana hakikanin ma'ana ta tunanin "Mayar da moriyar jama'a a gaban komai". Tun daga jariri da bai wuce sa'o'i 30 da haihuwa ba, zuwa tsoho dake da shekaru fiye da 100 a duniya, Sin ta yi iyakacin kokarin ceton rayukansu, duk da ganin sadaukarwar da aka yi.

Kamfani mai ba da shawara mafi girma a duniya wato Edelman, ya ba da wani rahoto a watan Maris cewa, yawan jama'ar kasar Sin da suke da imani kan gwamnatin kasar ya kai kashi 90%, adadin da ya kai matsayin farko a duniya a cikin shekaru 3 a jere. Wannan shi ne babban goyon baya da jam'iyyar mai mulkin kasar Sin ta samu.

Yayin da aka shiga sabon zamani, an yiwa JKS gyaran fuska bisa jaruntaka da ba a taba ganin irin ta ba, ta yadda za ta gudanar da harkokin jam'iyya bisa manufofi masu tsanani, matakin da ya sa ta samu ci gaba mai yakini a cikin tarihi, abun da kuma ya samar da tushe mai inganci wajen cimma burin raya tattalin arziki, da kuma al'ummar kasar.

Abin lura shi ne, JKS ba ma kawai tana kokarin farantawa jama'a rai ba ne, har ma tana mai da hankali kan makomar Bil Adama. Ya zuwa yanzu, an shigar da tunanin raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, a cikin kudurorin MDD sau da dama, kaza lika, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta samu karbuwa matuka a duk fadin duniya. Matakin da ya bayyana cewa, JKS ta hada raya kanta da duniya waje guda, abun da ya bayyana matsayin da take dauka na sauke nauyin dake wuyanta, wajen tabbatar da makomar Bil Adama mai haske. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China