Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kaddamar da shirin gaggawa na tallafawa yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa
2020-06-29 12:49:31        cri

Sin ta kaddamar da shirin gaggawa bisa mataki na 4, na tallafawa yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa, bayan da mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya, a yankunan tsakiya da kudu maso yammacin kasar.

A cewar ma'aikatar samar da daukin gaggawa ta kasar ko MEM, matakin na 4 shi ne na karshe a jerin matakan gargadi game da aukuwar iftila'i.

Ma'aikatar wadda ke samar da agaji ga al'ummun da bala'u suka auka musu, ta aike da tawagar musamman ta ma'aikata, zuwa yankunan lardunan Sichuan, da Guizhou da kuma Hunan, don ba da gajoranci ga ayyukan jin kai.

Tun daga farkon watan Yunin nan kawo yanzu, ambaliyar ruwa ta shafi kusan kimanin mutane miliyan 12, yayin kuma wasu mutanen 78 ko dai suka rasu ko suka bace. Kaza lika bala'in ya rushe gidaje 8,000, baya ga wasu 97,000 da suka lalace a yankunan lardunan kasar 13.

Rahotanni daga ma'aikatar ta MEM na cewa, asarar da aka yi sakamakon ambaliyar ruwan ta kai ta kudin Sin biliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 3.64. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China