Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kara fahimtar al'adun bikin Duanwu yayin da ake dakile COVID-19
2020-06-28 19:07:22        cri

Ranar 25 ga watan Yunin shekara ta 2020, wato ranar 5 ga wata na biyar bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, rana ce ta bikin Duanwu, daya ne daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na al'ummar kasar Sin, kuma tarihinsa ya wuce shekaru dubu 2. Game da asalin bikin na Duanwu, akwai tatsuniyoyi da dama, inda wasu suka ce domin bautawa gunki, wasu suka ce domin tunawa da kaka da kakanninmu, wasu ma suka ce domin tunawa da wani marubucin wake-waken kasar mai kishin kasa wanda ake kira Qu Yuan.

Kamar sauran wasu bukukuwan gargajiya na kasar Sin, bikin Duanwu na da al'adu masu tarin yawa, inda cin Zongzi da wasan kwale-kwale suka fi muhimmanci. Zongzi wani nau'in abinci ne, wanda aka yi shi ta hanyar kunsa shinkafa mai yauki da dangin gyada cikin ganyaye sa'annan a dafa shi a ci. Wasan kwale-kwale ko kuma wasan Dragon Boat shi ma wani muhimmin aiki ne mai ban sha'awa da jama'a kan yi a yayin bikin Duanwu, abun da ya sa ake kuma kiran Duanwu da sunan Dragon Boat Festival.

Amma sakamakon annobar COVID-19, yadda al'ummar kasar Sin suka gudanar da bikin Duanwu na bana ya bambanta da na shekarun baya. Alal misali, a bana, maimakon jama'a su taru a waje guda, sun yi yawon shakatawa ne ta hanyar kallon hotuna ko bidiyo ta kafar sadarwar Intanet, al'amarin ya kara ba su damar zurfafa fahimta kan nagartattun al'adun na bikin Duanwu.

Hakikanin gaskiya, cin Zongzi da wasan kwale-kwalen na Dragon Boat ba kawai al'adun gargajiyar bikin Duanwu ba ne, har ma ana samun sauran wasu al'adun da suka shafi kiwon lafiya, kamar rataye wasu nau'o'in ganyaye a gida ko sanya wasu kananan jakunkunan dake dauke da maganin gargajiya a jiki da dai sauransu. Duk da cewa hanyoyin da muke bi wajen shawo kan annobar COVID-19 a halin yanzu sun bambanta da na lokacin baya, amma manufarsu kusan iri daya ce, wato dora muhimmanci kan kare lafiyar dan Adam. Ko da yake ayyukan kandagarkin cutar COVID-19 suna haifar da dan tsaiko ga zaman rayuwar al'ummma a halin yanzu, amma za'a kara fahimtar ainihin abubuwan dake tattare da al'adun bikin Duanwu.

Domin hana yaduwar cutar COVID-19, a yayin bikin Duanwu na bana, duk da cewa ba mu iya haduwa a waje guda don kallon gasar tseren kwale-kwale ba, amma muna iya zama tare da iyalinmu a gida don samar da abincin Zongzi. Duk da cewa ba mu iya yin yawon bude ido a wurare masu nisa ba, amma muna iya bayyanawa yaranmu tatsuniyoyin da suka shafi asalin bikin, musamman wadanda suka shafi marubucin wake-waken nan dan kishin kasa mai suna Qu Yuan.

Haduwa da iyali, da cin abincin gargajiya, don kara fahimtar nagartattun al'adun gargajiya na bikin Duanwu, ya sa duk inda al'ummar kasar Sin suke, za su iya yin bikin cikin armashi da annashuwa. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China