Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi garkuwa da wasu jami'an ba da agaji a Nijar
2020-06-26 14:13:31        cri
Rahotanni daga janhuriyar Nijar na cewa, wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da ma'aikatan wata kungiyar ayyukan jin kai mai zaman kanta, da yawan su ya kai a kalla 10 a jiya Alhamis.

An yi garkuwa da jami'an agajin ne a yankin Tirabe, dake daf da yammacin iyakar kasar da kasashen Mali da Burkina Faso. A baya bayan nan dai ana samun yawaitar hare-haren mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda, dake ikirarin goyon bayan kungiyar IS a wannan yanki, lamarin dake haifar da asarar rayuka masu yawa. (SAMINU)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China